MUHAMMAD TAJAJJINI ƊAN TIJJANI
Kisan da Sojijin ƙasar nan suka yi wa Musulmi ‘yan bikin Maulidi a Tudun Biri dake ƙaramar hukumar Igabi a Jihar Kaduna ta hanyar jefa musu bom har sau biyu wanda hakan ya jawo asarar rayuka wajen 100 kuma ya jikkata dubbai abin Allah wadai ne.
Na ji da yawa wasu na kwatanta irin yadda za ta kasance da wannan ganganci da rashin hankalin ya faru a kudancin Najeriya bori da tanshintashinan da zai biyo baya daga matasansu da kafofin yaɗa labaransu na rashin yarda ko kaɗan da al’amarin.
Wasu a nuna rashin jin daɗinsu na shiru da suka ji masu mulki, manyan ‘yan siyasa, masarautu, malaman boko da na Islama, manazarta, fitattu, sanannu a kowanne fage na rayuwa, masu fashin baqi da uwa uba kafofin yaɗa labarai na Arewa suka yi a kai.
Suke cewa da a Kudu hakan ta faru da gaba ɗaya da kakkausar murya za su yo can su ruɗa ƙasar ta hanyar amsa amon kokawa da ƙorafin dole a yi maganin ta’addanci da aka tafka wa waɗannan bayin Allaah da aka raba su da rayukansu ba su ji ba su gani ba.
Za kuma su ajiye duk wasu bambance- bambancen dake tsakaninsu da dukkan abinda suke yi komai muhimmancinsa a gare su su ci gaba da ruruta wutar zancen har sai duniya ta ji sannan a nemi ba’asi har ta kai Amurka, Turai da ko’ina su nemi a yi wa waɗanda aka zalunta adalci a biya su diyya.
Bugu da ƙari shi ne, wasu suka kama ƙorafin rashin buɗe kafafen yaɗa labarai a wajen manyan Arewa suna cewa da an kakkafa su da mu ma za mu samu murya ɗaya ta isar da saƙonninmu yadda duniya bakiɗaya za ta dinga jin menene damuwar Arewa da al’umarta.
A wannan gava ne na fito nake yi musu bayani cewa ba buɗe kafofin yaɗa labaran ba ne matsalar ba amma dalilin buɗe su shi ne ginshiƙi. Sau da dama ana kafa gidajen radiyo da talabijin da jaridu ne saboda wasu muhimman dalilai
Mafi akasarin kafafen yaɗa labarai a Arewa ba a buɗe su da manufar waɗannan dalilai wato kare haƙƙi da kwatar yanci, kare addini, hana gurɓata harshe, bunkasa al’ada, sayar wa duniya gargajiyar al’uma, kare wa yanki haƙƙinta da dai makamantansu.
Sai dai a nan Arewa da yawa-yawan kafofin aikin jarida ana kafa su don kusan abu biyu ko uku. Ga su kamar haka: Na farko kare mutumcin kai da samun kafa ta mai da martani ga ‘yan hamayya ko ‘yan adawa da duk wani wanda aka ɗauka maƙiyi ne.
Na biyu saboda kasuwanci, neman kuɗi ko jari hujja. Muddun kuɗi za su samu daga gudanar da harkar sadarwa da isar da saƙo to duk wani abu na tsare martabar al’uma ko shiyya ko ɓangare baya cikin lissafi sai dai ko ya zama ɗan karere ko ya yi rakiyar nufi.
Sannan na uku saboda ya zama mabuɗin shiga kofofin duk inda mai kafar yaɗa labaran zai iya shiga don nemawa kansa a karon farko wata dama daga masu mulki, manyan ‘yan kasuwa, masu faɗa aji cikin al’umar ƙasar ko yankin kai ko ma duniya.
Shi ya sa za ka ga da yawa kafofin sadarwarmu a Arewacin Najeriya irin wannan cin mutumci, tozarta mutanenmu, danne haƙƙinmu a majalisa, rajin kare haƙƙin bil Adama, tauye wa ‘yan shiyyar damarmakinsu a wajen ɗaukar aiki, rabata dai-dai a dukiyar ƙasa da dai sauransu duk ba su dame su ba.
Baya da wannan in an bi ta varawo to a bi ta ma bi sawu. Akwai ‘yan Arewa da dama a Soshal Midiya in kuka duba shin kishin al’umarmu yana daga cikin abinda yake damunsu ko aƙidarsu ko manufar kasancewarsu a kafofin sada zumanta?
A haƙiƙanin gaskiya da dama a cikinmu nema wa al’umarmu haƙƙinta ba ya daga cikin aniyarmu na hawa soshal midiya. Abin da mafi yawancinmu suka sa a gaba shi ne nishaɗi, barkwanci, sharholiya, soki burutsu, bambadanci, tumasanci da dai ire-irensu.
Ba za ka ga wani abu da ya shafi ƙwatar wa jama’armu kasonsu ko yaye musu ƙunci ko yaƙar rashin adalcin da ake nuna musu ‘yan dandali intanet sun yi rubutu ko dogon bayani ko bidiyo ko shiyarin ko sharhi ko fashin baqi ko tambihi da makamantansu a kai ba.
Duk wanda yake da ja ya je ya yi bincike a TikTok, Fesbuk, Instagiram, Tuwita, Waz’af da sauransu ya ga menene y’an Arewa suka mai da hankalinsu kai kama daga kallo, ɗora kwanten wato ƙirƙira, saukewa daga shafuka za ku ga wAllaahi shiririta ce.
To yanzu a hakan shi ne sauran mutan duniya za su ɗauka mun damu da kanmu, rayuwarmu, ci gabanmu da nemawa kanmu kima da daraja? Ku taya ni dubawa don Allah. Wannan na daga cikin dalilan da ya sa kowa ma yake ganin damar duk wani mutumin Arewa ba a bakin komai yake ba.
Tijjani M. M., DWi, SWS Radio Rangaɗaɗau, marubuci ne kuma mai sharhi a kan al’amurra yau da kullum musamman na siyasa da zamantakewa. Ya rubuto daga jihar Kano.
