Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Ƙungiyar mutanen Ebira a jihar Kebbi ta bai wa Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi lambar yabo. bikin bajekolin al’adu da karramawar jama’a wanda ya gudana a jiya a ɗakin taro na Saffar da ke Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi.
Da yake jawabi a wajen taron da ya halarta, shugaban ƙungiyar Malam Suberu Asuku Iliyasu ya bayyana karramawar ga Maigirma Gwamnan ya samu kyakykyawan sakamako bisa la’akari da ci gaba da haɗin kai da ya kawo jihar Kebbi tun bayan hawansa karagar mulki watanni bakwai da suka wuce. Ya ƙara da cewa an nuna hakan ne ta hanyar naɗa wasu muqamai masu muhimmanci a jihar.
Kwamishanan yaɗa labarai da al’adu na jihar Kebbi, Alhaji Yakubu Ahmed BK wanda ya wakilci gwamnan a wajen bikin kuma ya samu lambar yabo, a madadinsa, ya bada tabbacin ƙungiyoyin raya ƙasa da al’adu dake zaune a jihar Kebbi kan tsaron lafiyarsu da kuma bada gudummuwarsu wajen ganin an mayar da jihar nan gaba.
Ya gode wa ƙungiyar mutanen Ebira bisa ganin gwamnan ya dace da wannan lambar yabo tare da yin kira ga sauran ƙungiyoyi irinsu da su haɗa kai da kansu cikin al’ummar jihar Kebbi, ta hanyar shirya al’adu tare da nuna kimarsu.
Mahalarta taron sun haɗa da shugaban ma’aikatan gwamna Barista Attahiru Maccido, kwamishinan matasa da wasanni Kwamared Nura Fingilla, Bunun Gwandu Ibrahim Sarkin Kudu, wanda ya wakilci Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar, Hakimin Ambursa Alhaji Isa Haruna Rashid da sauransu da dama.
