Daga AMINA YUSUF ALI
Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya fara kaddamar mataki a kan rahoton da mai bincike na musamman na Babban Banki Nijeriya (CBN) da sauran abubuwan da suka dangance shi, Jim Obazee ta hanyar rushe shugabancin gudanarwa na Bankin Titan Trust da wasu guda uku.
Majiyarmu ta bayyana ragowar bankunan da aka kaddamar wa wannan hukuncin kansu sun hada da Bankunan Union, Polaris, da kuma Keystone.
The kwamitin daraktoci da shugabannin zartarwa na bankunan an gayyace su wani taron ganawa a ranar Larabar da ta gabata 10 ga watan Janairu 2024 inda mataimakin CBN a bangaren tsarin kudi Phillip Ikeazor, ya yi musu jawabi na tsahon mintuna 30 kowannensu.
Sauran mataimakan gwamnan Babban Bankin da suka yi cikin kwamitin taron sun hada da mataimakin gwamna a bangaren gudanarwa, Emem Usoro, mataimakin gwamnan a bangaren tsarin tattalin arziki, Muhammad Abdullahi da kuma mataimakin gwamnan a bangaren, Bala Bello.
Kwamitin ya bayyana matsaloli na rashin biyayya ga hukuma da saura laififfuka da bankunan da abin ya shafa suka aikata sannan sai suka kori ma’aikatan a hukumance.
Wannan lamari da ya faru dai ya biyo bayan rahoton wani bincike da mai bincike na musamman na CBN da madangantansa, Jim Obazee ya gudanar.
Idan ba a manta ba, mai bincike na musamman da shugaba Bola Tinubu, ya nada ya tava gayyatar masu hannun jari a bankin Titan Trust wani taro amma rahotanni sun nuna cewa sam ba su mutunta gayyatar da ya yi musu ba na halartar taron ganawar da mai binciken na musamman.
Ana sa ran dai Babban Bankin Nijeriya CBN zai wallafa jawabi a game da lamarin a hukumance nan ba da jimawa ba.
