MOPPAN ta taya Ali Nuhu murna kan sabon naɗin da Tinubu ya yi masa

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar shirya finafinai ta MOPPAN ta nuna farin cikinta tare da taya murna ga jarumi Ali Nuhu dangane da naɗin da Shugaba Bola Tinubu ya yi masa a matsayin Shugaban Hukumar Finanai ta Kasa.

Sakon taya murnar na kunshe ne cikin wasiƙar da kungiyar ta aike wa jarumin mai dauke da kwanan wata 12 ga Janairun 2023 da kuma sa hannun Shugaban Kungiya na Kasa, Ahmad Sarari.

Wasikar ta ce, “Muna taya ka murna dangane da nadin da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya yi maka a matsayin Manajin-Darakta na Hukumar Finanai ta Nijeriya.

“Muna matukar alfahari da nasarorin da ka samu da suka zama abin koyi a masana’antar shirya fina-finai.

“Mun yi amannar nadin da aka yi maka zai bunkasa Masana’antar Finanai ta Nijeriya. Muna fatan Allah Ya kare ka, Ya kuma yi maka jagora wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanka.

“Mun yaba da kokarinka wajen ciyar da harkar fim gaba a Afurka, musamman masana’antar Kannywood. Muna alfahari da kai bisa nassrorin da ka samu da kuma martabawsr da ka kawo wa Kannywood.

“Vodiya muke da fahimtarka da kuma jajircewarka da kuma kasancewarka abin koyi ga matasan Nijeriya, musamman natasan Arewa da baki dayanmu a kungiyar MOPPAN,” in ji wasikar.

By Editor