Sanata Barau zai jagoranci kafa cibiyar zamani ta horar da jami’an shige-da-fice a Bichi

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Tarayyar Nijeriya, Sanata Barau I. Jibrin zai kafa cibiyar horas da jami’an shige da fice ta kasa (NIS) a karamar hukumar Bichi da ke shiyyar jihar Kano ta Arewa. 

Sanata Barau ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis yayin da Kwanturola-Janar na hukumar NIS, Wuraola Adepoju, ta kai ziyarar ban girma zuwa ofishinsa a majalisar dokokin tarayya dake Abuja.

A cikin wata sanarwar manema labarai da mai ba shi shawara akan harkokin yada labarai Ismail Mudashir ya fitar, Sanata Barau ya bayyana yunkurinsa kan samar da cibiyar horaswa ta zamani. 

“An tuntube ni a makonnin da suka gabata kan yiwuwar kafa cibiyar horar da jami’an shige da fice ta zamani a Bichi, Kano ta Arewa, kowa ya san mahimmancin hukumar ga kasarmu, ya zama wajibi a tallafa wa wannan hidima don amfanin dukkan ‘yan kasa.

“Bisa wannan ne nake tabbatar muku cewa ofishina zai taimaka wajen samar da cibiyar horaswa tun daga farko zuw karshe, da yardar Allah za mu tabbatar da an gina ta tare da samar da kayan aikin horar da ma’aikatan hukumar da kuma horar da su,” in ji shi.

Sanata Barau ya kara da cewa, bayan an kafa cibiyar, za ta sanya hukumar ta NIS a matsayi mafi kyau don yin aiki tukuru.

Za a samar da cibiyar ne a karamar hukumar Bichi dake shiyyar Kano ta Arewa.

Da take yaba wa Sanata Barau kan wannan aiki Wuraola ta ce, “Muna matukar godiya da wannan aikin, ba shakka horarwa na da matukar muhimmanci wajen bunkasa ma’aikata, idan ba a samu ingataccen horo ba, duk ingancin kayan aiki ba za a samu aiki ingatacce ba,” inji ta.

By Editor