Daga BASHIR ISAH
Jami’an tsaro a jihar Bauchi sun kama wani dalibin Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa University (ATBU) Bauchi bisa zargin mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba.
Kakakin Rundunar ‘Yansandan Bauchi, Ahmed Wakil, ya bayyana a ranar Laraba cewa, an tsare dalibin ne a ranar Asabar da ta gabata bayan da ‘yan bijilanti suka kwarmata musu cewa dalibin ya mallaki karamar bindiga kirar gida har da alburushi.
Ya ce tuni dalibin wanda dan aji hudu ne a ATBU ya amsa laifin da ake zarginsa.
Ya kara da cewa, wanda ake zargi ya yi ikirarin asali bindigar ta wani ce wanda shi ma aka kama shi da laifin mallakar bindiga ta haramtacciyar hanya a 2021.
Wakil ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin bayan sun kammala bicike.
