Majalisar Kolin ta ce ta sami kwarin gwiwar jaddada goyon bayan nata ga Shugaban Kasa Bola Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ne biyo bayan hukuncin da Kotun Kolin ta Nijeriya ta yanke kan raba gardamar zabe inda kotun ta tabbatar da Shugaba Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben na shekarar 2023.
Majalisar ta ce hukuncin ya kara tabbatar da cewa zaben da majalisar ta yi ba na tumun-dare ba ne don ya dace da zabin ‘yan kasa.
A cikin wata sanarwa da Majalisar ta fitar a wajen taronta na kasa na yini biyu da aka gudanar a Abuja, Majalisar ta jaddada cewa goyon bayansu ga tikitin takarar shugaban kasa biyo bayan fifita cancanta a kan sauran batutuwa da kungiyar ta yi da nufin ciyar da Nijeriya gaba.
Bugu da kari, Majalisar ta yi karin haske kan yadda gwamnatin ke gudanar da ayyukanta, lamarin da ke nuni da cewa a halin yanzu galibin ‘yan Najeriya masu kishin kasa sun fahimci irin ci gaban da zaben wannan tikiti ya samar wa kasa maimakon takure shi a matsayin tikitin addini zalla.
Majalisar SCSN ta kuma mika cikakken goyon bayanta ga shirin gwamnati na yaki da cin hanci da rashawa da nufin inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.
Daga nan ta shawarci Shugaba Tinubu da ya fifita daidaito da adalci da cancanta wajen nada mukamai da gudanar da mulki domin nuna sahihancin gwamnati wajen inganta rayuwar ‘yan kasa.
A bangaren tsaro, Majalisar ta yi kira da a samar da ingantacciyar hanyar tattara bayanan sirri, da ci gaba da kai farmaki kan ‘yan ta’adda, tare da inganta aikin ‘yan sanda domin maido da zaman lafiya a sassa daban-daban na fadin kasar nan.
SCSN ta kuma yi kira da a sake duba kundin tsarin mulkin kasar domin bai wa gwamnoni damar tafiyar da al’amuran tsaro yadda ya kamata a jihohinsu tare da yin Allah wadai da kashe-kashe da hare-haren da ake kai wa a fadin kasar nan, inda ta bukaci gwamnati da ta kaddamar da cikakken bincike tare da gurfanar da wadanda aka kama da irin wadannan laifuka gaban doka.
A karshe, Majalisar ta yaba wa gwamnatin tarayya kan yadda ta ke ci gaba da yakar kungiyar masu auren jinsi ta LGBTQAI+ a Nijeriya tare da yin kira ga al’ummar musulmi da su koma ga Allah da gaske tare da yin kira ga malaman addinin musulunci da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na jagoranci da kuma hada kai wajen yi wa shugabannin kasar addu’a domin magance matsalar rashin tsaro da matsin tattalin arziki da ke addabar kasar a halin yanzu.
