Tsaro: Gwamnan Zamfara ya haramta wa sarakunan gargajiya bada izinin haƙar ma’adina

Daga BASHIR ISAH

A matsayin mataki na ci gaba da yaki da matsalar tsaro a Jihar Zamfara, Gwamnan Jihar, Dauda Lawal, ya rattaba hannu kan dokar da ta haramta wa sarakunan gargajiya a fadin jihar bai wa masu hakar ma’adinai izinin gudanar da harkokinsu a jihar.

Lawal ya ba da wannan umarnin ne yayin taron Majalisar Zartarwa na Jihar da ya gudana a Fadar Gwamnatin Jihar a ranar Alhamis.

Mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar ran Alhamis cewa, an ba da wannan umarni ne domin dakile matsalar ‘yan fashin dajin da ke ci wa jihar tuwo a kwarya.

A cewarsa, dokar ta haramta bada wasikar izini kowace iri ga daidaikun mutane da kamfanoni ko hukumomi masu hakar ma’adinai a jihar.

Sa’ilin da yake jawabi a wajen rattaba hannu kan wannan doka, Gwamna Lawal ya jaddada cewa an dauki wannan mataki ne saboda hatsarin da ke tattare da bada wasikar izinin barkatai

“A kokarin da gwamnatina ke yi wajen yaki da matsalar tsaro, na ba da umarnin haramta wa sarakunan gargajiya bayar da wasikar izini ga masu hakar ma’adinai a yankunan kananan hukumomi 14 da Zamfara ke da su.”

Gwamnatin jihar ta ce ta gano ayyukan masu hakar ma’adinai na daga manyan abubuwan da ke tsananta matsalar tsaro a Zamfara, musamman ma matsalar ‘yan fashin daji.

“A matsayin gwamnatin da ta san ciwon kanta, ya kamata mu dauki ingantattun matakai wajen dakile hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba da ke rura wutar matsalar tsaro.

“Wannan ne ya sa na rattaba hannu kan dokar hani. Muna daukar matakan da suka dace wajen warware matsalolin da suka dabaibaye batun bada wasikar izini wanda ake yi wa rikon sakainar kashi.

“Muna rokon Allah Madaukaki da Ya ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a,” in ji Gwamna Lawal.