Wasan farko na Maroko yana nuna karsashin ƙungiyar na lashe gasar AFCON – Rahoto

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

kungiyar Kwallon Kafar Kasar Maroko da ta girgiza duniya a 2022 da ta kai wasan daf da na karshe a gasar kofin duniya, ta samu nasarar doke Tanzania da ci 3-0 a kan ‘yan wasa 10 a ranar Laraba a gasar kofin nahiyar Afirka, wanda hakan ke nuna karsashin kungiyar na lashe gasar Kofin Nahiyar Afrika.

Kyaftin Romain Saiss, Azzedine Ounahi da Youssef En-Nesyri duk sun ci wa Morocco kwallo a birnin San-Pedro da ke gabar tekun Ivory Coast, yayin da Tanzania ta kori Novatus Miroshi.

Duk da cewa kasar Maroko ta kasance kasa mai karfin fada aji a Afirka tsawon shekaru da dama, Maroko na neman lashe kofin gasar na biyu ne kawai, shekaru 48 bayan dauke kofin a Habasha.

Maroko ta yi fice a duniya sama da shekara guda da ta wuce a Katar lokacin da ta zama ta farko a gasar kofin duniya na Afirka da ta yi waje da Spain da Portugal a kan hanya.

An yi hasashen nasarar da za ta yi a rukunin F a wajen Tanzaniya a ranar Laraba, yayin da ta ke matsayi na 13 a duniya, da matsayi 108 a saman Taifa Stars.

Maroko ta fara ne da bakwai daga cikin ‘yan wasan da suka fara a gasar kofin duniya da suka tashi 2-0 a wasan kusa da na karshe a hannun Faransa a Katar.