Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Adadin wadanda suka mutu sakamakon fashewar wani abu da ya afku a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, a ranar Talata, 16 ga watan Janairu, ya kai mutum biyar.
A ranar Laraba da daddare, gwamnan jihar, Seyi Makinde, yayin da yake bayar da karin haske a gidan talabijin na Channels Television a wani shirin siyasa mai taken “Politics Today”, ya ce an samu mutuwar mutane biyu a ranar Talata, inda ya qara da cewa wani wanda abin ya shafa ya mutu a asibiti ranar Laraba.
Sai dai a wani sabon rahoto da aka fitar a ranar Alhamis, mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin tsaro, Seyi Makinde, Fatai Owoseni, ya ce an sake gano wasu gawarwaki biyu.
“Har yanzu ana ci gaba da aikin ceto. Ya zuwa jiya, mun samu mutum uku da suka mutu, amma da safiyar nan, kusan mintuna 30 da suka wuce, na samu labari daga jami’an tsaro da ke tallafa wa tawagar likitocin cewa an sake gano wasu gawarwaki biyu a safiyar yau,” inji shi.
Mai taimaka wa gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta tabbatar da hukunta wadanda ke da alaqa da wannan mummunan lamari kai tsaye ko kuma ta nesa.
Ya ce gwamnati tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro na tattara bayanan da suka kamata domin gujewa aukuwar makamancin haka nan gaba.
A cewarsa, hakan ne don gina amanar jama’a ga gwamnati tare da samar da gaskiya a harkokin mulki.
Owoseni ya ce: “An yi tattaunawa da dama, tare da cudanya da jama’a ta yadda za su ga fayyace abin da gwamnati ke yi.
“Hukumomin tsaro, musamman ‘yan sanda, DSS da ke samun goyon bayan rundunar sojojin Nijeriya ta EOD Unit, su ma suna tattara bayanan da ke tattare da juna domin tabbatar da cewa an gudanar da sahihin bayanai wajen gurfanar da su gaban kuliya don tabbatar da cewa duk wanda, ko dai kai tsaye, yana da alaka ta nesa ko ta kusa akan wannan lamarin sai an gurfanar da shi gaban kuliya.”
Hukumar kula da harkokin kasuwanci (CAC) na wani kamfanin hakar ma’adinai da aka tuhuma da fashewar wani abu a ranar Talata a yankin Bodija na jihar Oyo ya nuna wasu sunayen ‘yan kasashen waje a matsayin masu hannu, inji Gwamna Makinde.
Ya kuma ce daga cikin mutane 77 da ke kwance a asibiti, an sallami 60 da suka jikkata yayin da gwamnatin jihar ta ceto mutum daya daga wurin fashewar.
“Mun gano mutum guda da rai a yau (Laraba) a karkashin baraguzan ginin. An sallami 60 daga cikin 77 da aka kwantar a asibiti.
“Muna qoqarin bankado sunayen mutanen. Mun yi ‘yan bincike-bincike kan kamfanin da abin ya shafa kuma a, haqiqa akwai wasu sunaye na ‘yan kasashen waje a cikin takardun CAC na kamfanin da abin ya shafa.”
Makinde ya ce jihar ta gano wani mutum wanda akwai buqatar jami’an tsaro su gayyato shi domin yi masa tambayoyi.
Gwamnan ya ce binciken farko da jami’an tsaro suka gudanar ya nuna cewa tashin bam din ya faru ne sakamakon wasu masu haqar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da suka mamaye daya daga cikin gidaje a Bodija, ya kara da cewa fashewar ta faru ne a kan titin Adeyi, Bodija. Sai dai kuma an ji kuma an ji shi a sassa da dama na birnin.
Ya ce, “Bincike na farko da jami’an tsaro suka gudanar ya nuna cewa masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da ke zama daya daga cikin gidaje a Bodija, sun ajiye bama-baman a can ne suka haddasa tashin bom. Ana ci gaba da gudanar da bincike. Duk wadanda aka samu da laifin haka za a gabatar da su gaban kotu.”
A halin da ake ciki, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin a gudanar da cikakken bincike don gano ainihin dalilin da ya haddasa fashewar.
