‘Yan gida ɗaya da aka yi garkuwa da su a Abuja sun shaƙi iskar ‘yanci

Spread the love

‘Yan matan nan ‘yan gida daya da aka yi garkuwa da su tare da mahaifinsu a yankin Abuja, sun shaki iskar ‘yanci.

A farkon watan Janairun da ake ciki ne ‘yan fashin dajin suka yi garkuwa da wadanda lamarin ya shafa, inda sakamakon jinkirin da aka yi wajen biyan kudin fansar da ‘yan bindigar suka nema, daya daga cikin yaran mai suna Nabeeha ta rasa ranta.

A karshen mako ne aka ga isowar ‘yan matan gidansu da ke Abuja bayan da aka ceto su daga hannun ‘yan bindigar.

Bayanai sun ce yaran sun koma gida ne bisa rakiyar jami’an tsaro inda iyayensu suka karbe su.

Kawun yaran, Sherifdeen shi ne ya tabbatar da sako yaran ga majiyarmu da safiyar Lahadin da ta gabata, inda ya ce a ranar Asabar aka sako yaran.

MANHAJA ta kalato cewa, duk da dai an biya fansar da ‘yan bindigar suka nema, duk da haka barayin dajin sun ci gaba da tsare yaran lamarin da ya jefa ahalinsu cikin zullumi.

Yaran da aka sakon sun hada da Najeeba da Nadherah da Habeeba da kuma Haneesa.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sherifdeen Al-Kadriyah, ahalin yaran da lamarin ya shafa sun nuna godiya ga ‘yan Nijeriya bisa taya su jimin halin da suka tsinci kansu.

By Editor