Kotu ta ayyana Kasafin 2024 na Jihar Ribas haramtacce

Spread the love

Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta  bayyana kasafin 2024 na Jihar Ribas a matsayin mara inganci kuma haramtacce.

Kotun ta haramta kasafin ne a zaman shari’ar da ta yi a ranar Litinin karkashun jagorancin Mai Shari’a James Omotosho.

A cewar Kotun, kasafin ya zama haramtacce ne saboda rashin ingancinsa da kuma saba tsari da aka yi kafin gabatar da shi a gaban Majalisar Dokokin Jihar.

Kotun, wadda ta ayyana Martin Amaewhule a matsayin halastaccen Shugaban Majalisar, ta kama Gwamna Fubara da laifin yi wa Majalisar Dokoki na jihar katsalandan cikin harkokinta.

Alkali Omotosho ya ce Gwamnan jihar ba shi da hurumin da zai tsoma bakinsa cikin harkokin Majalisar Dokin Jihar Ribas.

Kazaika, Kotun ta haramta wa Fubara ci gaba da kudurinsa na rushe ginin Majalisar Jihar Ribas, duk da dai ya ba da umarnin a sakar wa dukkanin kudadenta da suka makalea a baya.

By Editor