Gwamnatin Tarayya ta sahale wa kamfanoni bakwai da su rarraba man Ɗangote

Daga AMINA YUSUF ALI

A halin yanzu dai manyan kamfanonin dillancin mai guda bakwai da muke da su a Nijeriya sun yi rajista tare da kamfanin tace man Dangote domin rarraba tataccen mai ta hanyar sara da sarar da shi. Wato dai man fetur din da matatar Dangoten wacce aka gina ta a kan Naira biliyan 20 ta samar.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai su wadannan kamfannin dillancin a qarqashin shugabancin Kungiyar Manyan dillalan Man feturta Nijeriya (MOMAN) ita ce ta tabbatar da cewa,  bayan yin rajistar tasu, za su iya cigaba da rarraba man fetur din da aka samar a matatar bayan cimma yarjejeniyar cinikin a tsakaninsu.

Wannan bayani ya zo ne bayan Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Nijeriya (IPMA) suka ba da sanarwar cewa za su gana da mahukuntan matatar mai ta Dangote a wannan satin domin tattauna a kan cinikayyar man.

Haka kuma kungiyar mamallakan kamfanonin man fetur PETROAN su ne suke da alhakin tafiyar da sasanci da kamfanin tace man na Dangote da ya lashe biliyoyin Daloli.

A yayin da IPMAN suke PETROAN suke kokarin kulla alaka da matatar, su kuma mambobin MOMAN sun riga sun yi rajista da kamfanin kuma a shirye suke da su fara sayen kaya suna syarwa.

 Manyan kamfanonin bakwai da suka yi rajistar dillancin man sun hada da; 11 Plc, Conoil Plc, Ardova Plc, MRS Oil Nigeria Plc, OVH Energy Marketing Limited, Total Nigeria Plc da kuma NNPC Retail.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai matatar man ta Dangote ta sanar da fara samar da man gas wato dizel da kuma man JetA1 wato man jirgin sama. Hakan yana kunshe a cikin wani jawabi da shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya wallafa. A cikin jawabin an gode wa shugaba Bola Tinubu a kan gyon bayansa da karfafa gwiwa har wannan matatar ta kammala.