Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hedikwatar Tsaro ta sojoji ta bayyana aniyar ta na ganawa da Rev Timothy Daluk, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya a Karamar Hukumar Mangu ta Jihar Filato.
Daluk ya zargi sojojin Nijeriya da sa ido kan kashe-kashen Kiristoci da lalata dukiyoyi a jihar.
A wani faifan bidiyo da ya fito, Daluk ya yi zargin cewa sojojin Nijeriya na da hannu wajen kashe Kiristoci da varnata dukiya a jihar.
Ya yi ikirarin cewa sojoji na da hannu wajen korar Kiristoci tare da barin wasu gungun ’yan bindiga sun kona gidajensu a karamar hukumar Mangu.
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Filato ta yi kira ga hukumomin sojin kasar da su binciki zargin nuna son rai da ake yi akan sojoji a karamar hukumar Mangu, inda aka kashe mutane 30 a ranar Laraba.
Kwamishinan yada labarai na jihar Filato, Musa Ashoms, wanda ya bukaci hakan a wata hira da aka yi da shi ranar Laraba, ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su rungumi zaman lafiya.
