Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Matar Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Nafisa Nasir Idris Shugabar Gidauniyar NANAS Foundation ta kaddamar da gwaji da bayar da magunguna kyauta ga yara masu cutar Sikila guda dari biyu a jihar Kebbi karkashin gidauniyar NANAS Foundation.
Wannan tallafin zai zo ne karkashin hukumar bayar da tallafin kiwon lafiya Kebbi State Contributory Health Care Management Agency (KECHEMA).
Wannan hukumar ce za ta yi musu rajista sannan ta turasu a asibitoci mafi kusa da su domin cigaba da kulawa da su da kuma basu magunguna kyauta.a babban dakin taro na masaukin Shugaban Kasa da ke Birnin Kebbi.
Bayan kammala taron, hukumar ta KECHEMA ta karrama matar gwamnan bisa ga irin gudummawar da ta ke bayarwa musamman a vangaren marasa galihu.
Wata mai kama da wannan haka-zalika matar gwamnan ta ziyarci ofishin ma’aikatar kula da lafiya ta matakin farko, Primary Health Care da ke Birnin Kebbi inda ta kaddamar da sabon ofishin kungiyoyi na kasashen waje masu bada gudummuwa ta vangare daban-daban a jihar Kebbi a kan sha’anin kiwon lafiya.
Haka kuma ta qaddamar da sababbin motocin da aka kawo ga wadannan qungiyoyi domin ci gaba da aikinsu a nan Jihar Kebbi.
