Daga ABDULLAHI Sani Doguwa a Kano
An buƙaci masu hali da ke cikin alumar musulmi a ko’ina da su rinka tallafa wa kananan asibitoci masu zaman kansu da gudunmawar da ta dace, musamman asibitochin da ke duba larurar iyaye mata masu dauke da juna biyu, ko dai sauran alumma da suke da larurori daban-daban, duba da halin da alumma ke ciki na matsin tsadar rayu.
Mukaddashin babban daraktan lura da masu dauke da lafiyar iyali na asibitin Gabare Clinic & Maternity dake Sumaila, da ya bukaci a sakaye sunansa, shi ne ya yi wannan kira yayin ganawarsa da manema labarai.
Ya ce karancin kayayakin aiki na daya daga cikin matsalolin da kananan asibitoci ke fuskanta, tare da musanta zargin da ake yi kan cewa asibitoci masu zaman kansu na samun makudan kudade daga hannun alumma bayan yi musu aiki, lamarin da ya ce ba gaskiya ba ne.
Ya kara da cewa, Gabare Clinic na daga cikin asibitocin da ke bada gudunmawa wajen kula da marasa lafiya a yankin Sumaila da ke Jihar Kano, amma cewa asibitin na bukatar dauki daga masu hannu da shuni, ‘yan siyasa, kungiyoyi da sauransu don ci gaba da gudanar da harkokinsa na taimakon al’umma yadda ya kamata.
Wasu daga cikin ma’jinyatan da aka nemi jin ta bakinsu a asibitin sun yaba da kokarin wannan asibiti, tare da adduar fatan alheri.
