‘Yan sanda sun tabbatar da sace ‘yan rakiyar A’amarya 35 a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wata dabar ‘yan bindiga ta sace mata 35 a lokacin da suke dawowa daga rakiyar amarya a karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina da misalin karfe 8: 30 na daren ranar Alhamis.

Amma sai a wannan Litinin labarin ya yadu bayan da hukumomi suka ziyarci kauyen.

‘Yan bindigar sun yi wa motar ‘yan kai amaryar dirar mikiya inda suka harbi direman motar wanda yanzu haka yana kwance yana karbar magani.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Abubakar Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana cewar wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi kwanton bauna suka kuma sace mata kusan 35 dake komawa gida bayan rakiyar wata amarya zuwa gidan mijinta.

Kazalika, kwamishinan tsaro a jihar, Nasiru Mu’az ya bayyana wa manema labarai ce yawan matan da ‘yan ta’addar suka sace ya kai 53.

“Jami’an gwamnati sun ziyarci kauyen an kuma gaya masu cewa mutane 53 aka sace.

“Akwai hadari sosai a ce motocin ‘yan daukar amarya sun bi hanyar da ta yi kaurin suna wajen satar mutane kuma da daddare. Inji shi.

Daga qarshe kwamishinan ya bukaci al’umar jihar akan su daina tafiye tafiye cikin dare ya kuma ce gwamnatin jihar na bakin kokarinta don shawo kan matsalar tsaron da ta addabi wasu daga cikin kananan hukumomin jihar.

By Editor