Abin da ya faru a Minna aikin ɓata-gari ne ba zanga-zangar tsadar rayuwa ba – Gwamna Bago

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya ce dandazon jama’a da aka gani a kan hanya a wasu titunan garin Minna a ranar Litinin, ba zanga-zangar tsafar rayuwa ba ne face ayyukan wasu ɓata-gari ne masu neman daburta zaman lumanar al’umma.

Ya ce wasu bata-gari ne suka shirya dandanzon don samun danar wawure kayan abincin da wata mota ke da su wadda ke kan hanyar shigowa gari daga hanyar Bida.

Gwamnan ya kara da cewa, “Yanzun haka mun kama wasu daga cikin bata-garin kuma za mu ci gaba da daukar matakin ganin ba mu bari an kawo wa zaman lafiya da walwalar al’umma cikas ba.”

Bago ya bayyana hakan ne sa’ilin da yake ganawa da manema labarai abin da ya faru a babban birnin jihar a ranar Litinin.

Haka nan, ya ce sun kafa dokar hana siyan kayan abinci a manyan motoci a kasuwannin jihar, inda ya bai wa jami’an tsaro umarnin cafke duk wani ɗan kasuwan da aka kama da laifin boye abinci don haddasa wa al’umma kunci.

MANHAJA ta rawaito al’ummar garin Minna sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin dadinsu dangane da tsadar rayuwar da ake ci gaba da fuskanta a Nijeriya.

An ga masu zanga-zangar a ranar Litinin sun mamaye wasu manyan hanyoyin garin wanda hakan ya haifar da tsaikon zirga-zirgar abubuwan hawa.

Rahoto ya ce mazauna yinkin Kpakungu da ke Minna sun yi cincirindo a kan hanya daidai randabawul da ke yankin inda suka hana masu abubuwa hawa shiga da fita.

Bayanai sun ce jama’ar sun bukaci ‘yan sandan da suka bayyana a wurin don kula da dandazon da su hanzarta barin wurin ko kuma su gamu da fushin jama’a.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun daga kwalaye masu dauke da sakonni daban-daban kamar “Babu Abinci, muna mutuwa saboda yunwa” da dai sauransu.

Masu zanga-zangar sun kuma zargi masu rike da mukaman siyasa a jihar da rashin adalci wanda a cewarsu hakan ne ya jefa al’umma cikin halin kunci.