Matsalar da fyaɗe ke haifarwa ga ‘ya mace

Daga AISHA ASAS

Kafin komai zan so mu fara da bayyana ma’anar kalmar fyade kafin mu kai ga tattauna matsalolin da ake fuskata bayan fyaden.

Fyade wani nau’in cin zarafi ne ta bangaren jima’i, amfani da karfi yayin kusantar mace ko namiji, ma’ana yi ba da amincewar abokin tarayya ba.

Idan aka ce fyade, hankalin mutane ya fi tafiya ne ga mata, a ganin su mata ne kawai ake yi wa cin zarafi ta ɓangaren fyade. Ko kaɗan wannan zance ba haka yake ba, domin an tabbatar kaso 29 bisa dari na mazan duniya sun fuskanci cin zarafi ta ɓangaren fyade.

Hakan ba yana nufin adadin matan da ake yi wa fyade na daidai da na maza ba, domin na matan ya linka na mazan har da dori, dalilin kenan da ke sa ake ganin kamar mata ne kawai wannan musiba ke hawa kansu.

Bincike ya nuna cewa, yara kanana mata ne suka fi yawa a matan da aka fi yi wa fyade, yayin da manyan mata daga wuraren aiki kan samu wannan cin zarafi daga mazan da suke karkashin su a wurin aiki, sai kuma mata a masana’antun finafinai na duniya, kamar yadda a kwanaki da yawansu suka yaye labule kan irin fyaden da aka yi masu kafin kawowa matsayin da suke.

Haka ma za a iya samun kaso mai nauyi daga matan da suke gidajensu, wasu ta sanadin dirar ‘yan fashi a gidan, ko kwarto, ta hannun ‘yan’uwansu, ko kuma idan sun fita zuwa wani sha’ani.

Abin takaici da tashin hankali game da wannan musiba ta fyade, yadda har iyaye ake samu da aikata fyade ga ‘ya’yan da suka haifa da cikinsu.

Kamar yadda wani bincike da wata jaridar a nan gida Nijeriya ta yi, ta tabbatar iyaye 34 suka yiwa ‘ya’yan cikinsu 48 fyaxe a shekaru biyu da suka gabata, kuma adadin ya samu ne a jihohin 13 daga jihohin da muke da su.

Abin qarin tashin hankali kuwa, mafi rinjayi na daga wannan adadi kananan yara ne kuma mata, har da ‘yar watanni 15 da haihuwa, namiji ɗaya ne a wannan lissafin, yayin da aka samu manyan mata huɗu.

A taqaice dai abin nufi babu inda mace zata shiga ta vuya daga cin zarafi na fyaɗe, sai ga wadda Allah Ya kare.

Wasu masana sun bayyana fyaɗe a matsayin wani nau’i na matsalar kwakwalwa, domin ga wasu ko ga matansu ba sa samun gamsuwa matukar ba ta karfi suka yi masu ba. A wani vangare fyaɗe ga wasu tsabar rashin imani ne ko biyayya ga kwaya, ko neman duniya da zai sa ka karɓi dabi’ar a matsayin sharadi daga boka.

Bincike ya nuna, kaso mai yawa na mata musamman kananan yara daga Arewacin Nijeriya sun fuskanci wannan cin zarafi na fyade, sai dai da yawa daga ciki iyaye ko su karan kansu yaran na yin gum da bakinsu don gujewa rasa mijin aure, ko irin kallon da al’ummarsu za su yi masu.

Da wannan ne muke so mu gina darasin namu na yau, domin illar fyade ta fara ne daga lokacin da aka yi zuwa matakin da za a dauka.

Masana kwakwalwa sun tabbatar da cewa, fyade ba a iya al’aura illar sa ke tsayawa ba, asali ma idan da kulawa, akwai yiwar a iya kawar da matsalar ta wannan wuri cikin lokaci, (ga manyan mata, yayin da a ɓangaren kananan yara ya danganta da irin damejin da aka yi masu) sai dai matsalar tana tuma ne ta taɓa kwakwalwa, wannan zai sa tabon ya dauki shekaru bai gushe ba, kuma zai iya tasirin haifar da wata nau’in tabin hankali, wanda za su iya samun kansu a tsoron mu’amala irin wannan ko su dinga ganin za a yi masu ta karfi ne, har su kai ga kokarin illata abokin mu’amala tasu, a ganin su kare kansu suke yi.

Ta yaya fyade ke samun damar yin wannan illar?

A yayin da aka yi wa ‘yarki ko danki fyade, abu na farko da suke bukata shi ne, kai su asibiti don tabbatar da irin lahanin da aka yi masu, da kuma ba su taimakon da ya dace.

Idan an samu wannan, mataki na gaba da wanda aka yi wa fyade ke bukata shi ne, samun wanda za su sanar da shi abinda suke ji, kuma babu wadda ta cancanci wannan matsayi sai ke uwa.

Ki ba wa ‘ya’yanki damar fayyace abin da suke ji da kuma yadda suke so a yi game da wanda ya keta masu rigar mutunci. Koda kuwa kananan yara ne, ki ba su dama, domin hakan ma zai sa su amayyar da kuncin su, wanda zai rage masu nauyi a zuciya.

Mataki na gaba, bin hanyar da ta dace don kwatar masu hakkin cin zarafin da aka yi masu. Masana sun ce, hukunta wanda ya aikata fyade na daya daga cikin magungunan da ke samar da warakar zuci ga wanda aka yi wa fyaden. Sanin wanda ya aikata masu wannan tu’annati ya ɗanɗana kudar sa zai rage masu raɗaɗin a duk lokacin da suka tuna.

Ganin wanda ya yi masu fyaxe na walwala da rayuwa cikin jin dadi kawai zai iya hana wadda aka yi wa sakewa. Wannan kuwa kan samu bisa dalilai biyu, ko dai iyayen sun yi shiru don ba su so a san an yi wa ‘yarsu fyade, wanda hakan zai ba wa mai fyaden damar yin rayuwa tamkar bai aikata hakan ba. Ko kuma yanayin gurvacewar vangaren shari’a, ba wa mai laifi gaskiya don matsayi ko kuɗin da yake da su.

Duk da cewa, wasu lokuta ba a sanin ko alqalin zai yi adalci, dalilin ɓoye lamarin da iyaye ke yi, sakamakon gudun irin kallon da za a dinga yi masu, ko kuma yarinyar ta kasa samun mijin aure.

Wannna matsala na ɗaya daga cikin rashin adalci da al’umma ke yi wa matan da aka ci zarafin su ta fuskar fyade, musamman ma a Kasar Hausa. Da yawa akan nuna kyama maimakon tausayi ga macen da aka keta wa rigar mutunci, kuma hakan kan faru ne da masaniyar ba laifinta ba ne.

Idan aka yi wa yarinya fyade, kuma mutane suka sani, maimakon a taru a zame mata karfen da zai karfafa mata zuciya, a bata kulawa, a hada kai wurin kwatar mata hakkinta, a’a, kawai zata zama darasin tusawa a duk lokacin da aka hadu majalisa, zata zama abin nunawa a duk sa’ilin da ta wuce, za ta zama abin kyama a yayin da aka yi zancen mai auren ta.

Da wannan ne za ka tarar a unguwa daya an samu mutum ɗaya ya yi wa yara goma fyade, kuma yana zaune abinsa ba tsangwama bare kora, asalima ko uban yarinyar ba shi da halin faɗa da shi ko da na fatar baki ne. Dalili yana gudun a tambaye abinda ya haɗa su, har ta kai ga a fahimci fyade ya yi wa ‘yarsa.

Idan da al’umma za su cire kyama, su mayar da tausayi a gurbin ga wadda aka ci zarafin ta, da ya taimaka matuqa wurin rage yawaitar masu fyade musamman a Kasar Hausa, saboda ta hakan ne kawai za a iya ba wa iyayen wadda aka yi wa fyade damar daukar mataki.

Akwai al’umma a can cikin kasashen ketare da na tava jin labarin cewa, sun nemi dama daga hukuma kan a amince a ba wa kowane mai jagorancin kauyukansu damar iya yanke hukuncin fyade idan an kawo masa.

Da wannan aka ce, idan aka kama wani da laifin fyade, bayan an tabbatar, za a karbe wani kaso mai yawa na abinda ya mallaka a ba wa yarinyar da ya yi wa fyade, sannan a yi masa daddaka, kafin samarin garin su zaga da shi lungu da saqon garin don nuna shi a matsayin wanda ya yi fyade, aka hukunta shi, hakan zai hana shi samun matar aure, idan yana da aure, matarshi na da zavi na barin shi ta auri wani.

Mu kaddarta cewa, a al’ummarmu ake wannan hukunci, kuma ana yin adalci yayin hukunta talaka da mai kuɗi duk daya ne matuqar ka aikata laifin zai fuskanci irin wannan hukunci, ba na tunanin za a kai wannan lokacin ba a rufe babin fyade a tsakaninmu ba.

Kowa na da rawar da zai iya takawa ga rayuwar macen da aka yi wa fyade, tun daga iyaye ta hanyar bata kulawar da ta dace kamar yadda muka fada a baya, al’umma su daina kyama da bambanta ta da sauran mata, su daina gudun auren wadda aka yi wa fyade, su haɗa kai wurin ganin an kwatar mata hakkinta ko da hakan na nufin korar wanda ya yi fyaden daga cikin su, ko ba ku yi don Allah ba, ku yi don yayyafa wa gemunku ruwa yayin da na dan’uwanku ya kama da wuta.

Idan aka kasa samar da waxannan matakai ga macen da aka yi wa fyade, akwai yiwar ta taso da matsala a jikinta, wadda sai ta yi aure ne mijin ko ita za su iya fahimtar tana da ita, sakamakon rashin duba wurin a lokacin da aka yi fyaden, ko kuma ta rasa sha’awar namiji gabaxaya ta yadda sai ta dole mijinta zai kusance ta, wani sa’in ma za ta iya samun matsalar tsoron kusantar har a fara tunanin mutanen ɓoye ne suke tare da ita, sakamakon kai wa mijinta hari da ta ke yi a duk lokacin da ya yi yunkurin kusanto ta.