Alhassan Ɗantata: Mutum mafi arziki a Afirika ta yamma a shekarar 1950

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Alhassan Dantata, fitaccen attajiri a fadin nahiyar Afirika ta yamma, wanda tushen arzikinsa ya samo asali daga sayar da Goro da Gyada.

Haihuwa da nasaba;

Alhassan Dantata ya fito ne daga cikin zuri’ar Agalawa, iyayensa fatake ne masu yawon kasuwanci daga wannan gari zuwa wancan. An haife shi a shekarar 1877, a wani qaramin qauye da ake kira Danshayi a garin Bebeji, wanda ke da tazarar aqalla kilomita goma sha-biyar daga garin Kano. Alhasan daya ne daga cikin ’ya’yan Abdullahi wanda matarsa Fatima da ake kira Amarya ta haifa.

Shi Abdullahi da ne ga wani mutum mai suna malam Ali, wanda ake yiwa lakabi da Baba Talatin. Sun taso ne daga qasar Katsina da iyalensu kamar yadda suka saba, suka yada zango a garin Bebeji, bayan wani lokaci kuma sai Baba Talatin ya koma Madobi da zama, wanda a nan Allah ya yi masa rasuwa. Wannan dalilin ne ya zaunar da su a garin, wanda shi Abdullahi ya ci gaba da kula da iyalan har zuwa lokacin da suka kimtsa don ci gaba da tafiyar a shekarar 1877. Bayan sun shirya tsaf don tafiya izuwa garin Gonja, babbar cibiyar hada-hadar Goro ta kasar Ghana, sai matarsa Amarya ta haifi Alhassan a sansanin da suka yada zango a nan garin Bebeji.

Abdullahi mahaifin Alhassan ya rasu a shekarar 1885, lokacin Alhassan na da shekaru takwas a duniya, kuma yana da kanne kamar su; Malam Jaji, Malam Bala, Malam Sadi da sauransu. Duk suna kanana sosai a lokacin, don haka ba za su iya juya dukiyar mahaifin nasu ba.

Bayan an raba gado an ba wa kowa nasa kamar yadda shari’a ta tanadar, sai Amarya mahaifiyar Alhasan wadda dama ita ma tana kasuwanci kamar yadda mahaifiyar mijinta ke yi, ta yanke shawarar barin garin Bebeji inda ta bi ayarin fatake zuwa Accra ta kasar Ghana, inda a can ta ci gaba da yin kasuwancinta. Ta bar ’ya’yanta a Bebeji. Shi Alhassan ya kasance a qarqashin kulawar wata tsohuwar mata, wadda ta kasance baiwa ce, da ake kira da Tata. Alhassan ya samu duk wata kulawa da ake samu a wajen uwa, wannan dalilin ne ma ya sa tun a wancan lokacin ake kiransa da suna Alhassan Dantata.

Neman ilimi da gwagwarmayar rayuwar Dantata;

Alhassan Dantata ya yi karatun Alkur’ani (Allo) a nan garin Bebeji, makarantar da ke karkashin kulawar darikar Tijjaniyya. A matsayin almajiri yana da bukatar abinda zai taimaka wa kansa, wannan ya sa ya fara tsakurar abinda ya samu na daga gado domin ya tallafi rayuwarsa. A matsayin Almajiri mai daukar nauyin kula da kansa ta vangaren abinci da suture, har ma da tallafawa malaminsa, abu ne mai matukar wahala, don haka ya kan yi bara wani lokacin, wasu kuma su kan sanya shi aiki ya yi a biya shi. Aikin hannu, ko aikin karfi kamar wata al’ada ce ta matasan zuri’ar Agalawa da Alhassan Dantata ya gada. Hakan kuma bai hana shi samun lokacin yin karatu ba. Alhassan ya yi nasarar tara ’yan kudade a asusu, wanda Tata ke kular masa da shi.

Yana dan shekaru sha-biyar a duniya ya bi ayarin fataken Gonja, da niyyar kai wa mahaifiyarsa ziyara. Ya sari kaya a nan garin Bebeji ya tafi da su, wadanda ya sayar da fiye da rabi a hanyarsu ta zuwa Accra.

Ya yi farin cikin ganin mahaifiyarsa da yadda ya sameta cikin kwanciyar hankali, tare da bunkasar dukiyarta. Har ma ya yi fatan dukiyar za ta wadacesu su rayu tsawon lokacin da zai dawo ba tare da ya nemi kuɗi ba. Sai dai kwanansa ɗaya da zuwa sai ta dauke shi ta kai shi wajen wani malamin addini domin ya yi karatun Alkur’ani, tare da umartarsa da ya zauna a wajensa kafin lokacin tafiyarsa ya yi.

Dantata bayan karatun Kur’ani, a ranakun Alhamis da Juma’a yana fita neman aiki, ya yi sosai a Accra fiye ma da yadda ya yi Bebeji, haka kuma yana bawa malamin kaso mafi tsoka na duk kuxin da ya samu. Sannan yana yin barar abinci domin ya ci kuma ya kai wa malamin.

Bayan wasu ’yan kwanaki sai Alhassan ya dawo garin Bebeji domin ci gaba da neman ilimi, yayin da Tata ta ci gaba da dora shi a hanyar yin adani, inda ya ci gaba da ajiye kuɗi kullum a duk abinda ya samu.

Yadda rikice-rikice suka ritsa da Dantata;

A shekarar 1893 rikicin mulki da na fataucin bayi suka barke a garin Kano, lokacin Dantata yana da shekaru sha-shida a duniya. A lokacin aka samu wasu gungun marasa rinjaye da suka balle daga Kano, suka yiwa garin Bebeji tsinke, inda suka kori mutanen garin, suka karkashe wasu da dama, sannan suka kame wasu a matsayin bayi. Alhassan da ’yan uwansa Bala da Sadi, na daga cikin wadanda aka kama a matsayin bayi, daga baya Alhassan ya fanshesu da dukiya, suka shaki iskar ’yanci. Yanayin ya zowa Alhassan da tsauri a lokacin, saboda karacin shekarunsa.

Fadada harkokin kasuwanci;

Bayan rikicin ya lafa, sai Dantata ya mayar da hankalinsa kan shirye-shiryen fadada harkokin kasuwancinsa. Ya fara amfani da sabbin hanyoyin kasuwanci, inda ya fara zuwa Ibadan da Legas, tare da inganta dangantaka tsakaninsa da takwarorinsa ’yan kasuwa. Ya kan sayi dabbobi ya yi musu shaida ya loda su a katon jirgin ruwa ya rika kaiwa garuruwan; Accra, Kumasi, Sekodi, da Legas, daga can kuma ya saro goro ya kawo Kano ya rarraba wa kananan ’yan kasuwa. Shi ne dan kasuwa na farko a arewacin Nijeriya da ya fara habaka wannan hanyar kasuwancin, kuma ya dauki shekaru da dama yana yi. Wannan kokarin nasa ya jawo hankulan kasashen Turai wajen kulla dangantakar kasuwanci da shi.

Taimako;

Dantata ya taimaki mutane da dama rayuwarsa, ba iya kabilarsa ta Hausa ba, har da Yarabawa, da Inyamurai. Wadanda ya samar musu da aiki a kamfanoninsa, da ya ke biyansu. Haka nan da yawa daga cikin ma’aikanta musamman Hausawa suna kwana a gidansa, haka nan yakan dauki dawainiyar sha’ani na ma’aikatansa idan ya taso, kamar biki ko suna. Sannan ya kan shiga cikin ma’aikatansu su yi aiki tare, haka ma idan watamatsala ko rigima ta tashi a tsakaninsu, yakan shiga ya sasanta, kuma ya kashe rigimar.

Sanadin rasuwarsa;

A shekarar 1955 Dantata ya kamu rashin lafiya, ganin yadda cutar ta tsananta, sai ya tara ’ya’yansa, da mai kular masa da bangaren kudi, wato Garba Maisikeli, ya fada musu cewa shi fa rayuwarsa tazo karshe, babu abinda ya kamacesu su yi illa hadin kai. Ya ja hankalinsu da cewa, kar su bari wannan kamfanin na Alhassan Dantata and sons da ya gina, su bari ya rushe. Ya kuma roke su da su riki auren danginsu, su taimaki mabuqata, sannan su yi huldar arziki da sauran attajirai.

Kwanaki uku bayan wannan hudubar da ya yi musu, Alhasan Dantata ya rasu, a ranar Laraba 17 ga watan August 1955. A ranar aka binne shi a gidansa da ke Sarari. Ya rasu ya bar mata biyu, Umma Zariya, da kuma Maimuna. Daga cikin ’ya’yansa akwai; Mamuda Dantata, Ahmad Dantata, Sunusi Dantata, (wanda ya haifi Mariya, ita kuma Mariya ta haifi Aliko Dangote). Aminu Dantata, da kuma Mudi Dantata.