Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wani mai gadi a kwalejin Prestige International College, Nurudeen Shehu, mai shekaru 37, ya kashe kansa sakamakon labarin kara auren tsohuwar matarsa a Kano.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Usaini Gumel, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne a cikin daya daga cikin azuzuwan kwalejin a ranar Lahadi.
Gumel ya ce, “A ranar 28 ga watan Janairu da misalin karfe 10:30 na safe, Abdullahi Abdulsalam na Rijiyar Zaki ya ruwaito cewa an samu Shehu a rataye ba motsi a cikin aji.
“’Yan sanda daga sashin Gwale, karkashin jagorancin DPO, suka shiga cikin ajin, suka yanke igiyar, sannan suka garzaya da gawar zuwa babban asibitin Murtala Mohammed, inda wani likita da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa, sannan aka mika gawarsa ga iyalansa don binnewa.”
An tattaro cewa, labarin auren tsohuwar matar sa ne ya sanar da mumunan hukuncin da Shehu ya yanke na kawo karshen rayuwarsa.
Gumel ya yi alkawarin cewa rundunar ‘yan sandan za ta gudanar da cikakken bincike domin gano al’amuran da suka haifar da lamarin.
