Daga ISAH GIDAN ƁAKKO a Zariya
Babban limamin masallacin Abuja Farfesa Ibrahim Maqari Sa’id ya shawarci masarautar Zazzau ta ɗora ɗambar farfaɗo da gidajen ilimi da suka yi silar Zariya ta zama birnin ilimi fiye da shekara ɗari da suka gabata.
Farfesa Maqari ya bayar da wannan shawarar ce a lokacin taron Mauludin da ya saba jagoranta a ƙarƙashin shugabancinsa da taron ya gudana a fadar Zazzau.
Ya bayar da misalan wasu gidaje a birnin da ya ce a ciki da wajen Nijeriya a na zuwa Zariya domin neman ilimin addini na fannoni daban-daban da ɗan lokaci, sai wanda ya zo Zariya neman ilimin sai ka ga ya koma garinsu, ya zama malami, mai bayar da ilimi na fannin da ya karanta a Zariya.
Ya tabbatar da cewar in har masarautar Zazzau ta yunƙura domin farfaɗo da gidajen shi kansa da kuma wasu masana za su bayar da gudunmuwar da suka dace domin samun nasarar farfaɗo da waɗannan gidaje da suke birnin Zariya.
A dai majalisin da Farfesa Ibrahim Maqari Sa’id ya yi tsokaci kan yunƙurin mayar da babban masallacin Juma’a na fadar Zazzau ya ce wannan yunƙuri mai kyau ne, a cewarsa bai kai muhimmancin farfaɗo da waɗannan gidaje ba.
A saqonsa wajen taron mauludin, Mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli da Garkuwan Malaman Zazzau Malam Muhammadu Tukur Javva, ya yaba wa Farfesa Maƙari na yadda ya ke ayyuka da dama da suka zama silar ci gaban Musulunci a masarautar Zazzau da kuma Nijeriya baki ɗaya.
Game da kirar da Farfesa Maqari ya yi na farfaɗo da gidajen ilimi a Zariya, Garkuwan Malaman Zazzau ya ce, masarautar Zazzau bisa shugabancin mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli, an yi nisa na batun farfaɗo da waɗannan gidaje, kamar yadda ya ce, nan ba da jimawa ba ayyukan da fadar Zazzau ta sa a gaba kan waɗannan gidaje za su bayyana.
