A ranar Juma’a, ga ga Fabrairu aka ɗaura auren ‘yar Dokta Bilkisu Yusuf Ali, Sarrah Tasiu Yau da angonta Salhu Ibrahim Darma (Khalifa) a Kano.
An ɗaura auren ne a masallacin marigayi Imam Sheikh Dr. Yusuf Ali da ke cikin garin Kano bayan da aka sauko daga Sallar Juma’a.
Dokta Bilkisu shahararriyar marubuciya ce kuma malamar jami’a, kuma ‘ya ga Marigayi Imam Yusufa Ali.
Babban Editan jaridar Blueprint Manhaja, Nasiru S. Gwangwazo na daga cikin waɗanda suka shaida ɗaurin auren.
Sauran mahalartar sun haɗa da marubuta kamar Farfesa Yusuf Adamu, Bala Anas Babinlata, Larabi, Adamu Yusuf Indabo, Zahraddin Kallah, Lubabatu Yau, Maiturare, Kolo da sauransu.
MANHAJA na yi wa ango da amarya fatan rayuwa mai albarka.
Ga tsarabar hotuna daga wurin bikin auren:











