PDP ta ƙara ba Shugaban Matasan jam’iyyar na ƙasa dama a karo na biyu – Mannir Abdullahi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

An yi kira ga uwar Jam’iyyar PDP ta ƙasa, da ta ƙara bai wa Shugaban Matasan Jam’iyyar na Ƙasa dama a karo na biyu domin ƙara ƙarfafa wa matasa a sha’anin shugabanci.

Kakakin gamayyar ƙungiyoyin matasa na Arewacin Nijeriya, Kwamared Mannir Abdullahi Giwa shi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai jiya Alhamis.

Kwamared Mannir ya ce tunda aka ba Nijeriya ‘yancin kai a 1960 aka kuma fara mulkin dimukraɗiyya ba a tava shugaban matasa na kasa mai ƙoƙari da sanin makamar aiki kamar Prince Muhd Kadaɗe Suleiman ba, inda ya ƙara da cewa kusan jama’a ba su san mene ne aikin kujerar shugabancin matasa ba a cikin jam’iyya sai zuwan Prince Kadaɗe.

Ya ce a yanzu haka akwai jam’iyyu sama da hamsin a Nijeriya kuma inda kowace jam’iyar take da shugaban matasa na ƙasa amma a cewarsa babu wanda sunansa ake jin shi ko yake tashe a duk faɗin Nijeria kamarsa, saboda yadda ya fito da kujerar shugabancin matasa ta hanyar aikace-aikace da haɗa taruka don ci gaban matasa, a cewarsa.

“Haƙiƙa shugaban matasa na ƙasa na jam’iyyar PDP, Prince Kadaɗe ya buɗe sabon shafi a fagen siyasar Nijeriya, ɗaukacin matasan Nijeriya na masa godiya bisa fiddamu kunya da yake yi a kullum, yadda ya riƙe amana tare da ɗaukaka ofishinsa na shugaban matasa na ƙasa na jam’iyar PDP, shi ya sa a yanzu kam babu wanda ke shakkar cewa akwai wata dama ta kujeran shugabancin a ƙasar nan da matasa ba za su iya riƙewa ba.

“Da wannan muke ƙara kira da babbar murya a jam’iyar PDP mai albarka da ta ƙara bai wa wannan haziƙin matashi ɗan kishin ƙasa da jam’iyar PDP mai albarka dama domin qara ba shi dama a karo na biyu.”

Kwamared Mannir Abdullahi ya ƙara da cewa Prince Muhammad Kadaɗe haziƙin matashi ne wanda shigar shi cikin tsarin jam’iyya ya ƙara wa matasa qwarin gwiwa sosai wajen janyo hankalinsu domin shiga harkar siyasa dumu-dumu.