Matasa a Kano sun gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Matasa maza da mata da dama a jihar Kano sun fito domin gudanar da zanga-zanga don nuna adawarsu da tsadar kayan masarufi da ake fuskanta a Nijeriya.

Masu zanga-zangar dai sun fito ɗauke da kwalaye, inda suke rera waƙa mai taken “Tsadar rayuwa ba za mu iya ba”, a ƙoƙarin da suke yi na nuna halin da suke ciki.

Matasan waɗanda suka fito fuskokinsu a murtuke, sun gudanar da zanga-zangar ne a ranar Alhamis a unguwannin Bachirwa, Kurna da kuma Rijiyar lemo, da ke kan titin zuwa Katsina a Kano.

Kazalika, masu zanga-zangar dai sun ce rayuwa ta yi musu matuƙar wahala, a sakamakon yadda abinci yake neman gagarar su, balle a je ga sauran buƙatu na rayuwa.

Baya ga haka, sun ce kayan masarufi yana neman gagarar su, saboda yadda abubuwa da yawa suka ninka kuɗinsu sama da sau biyar, wasu ma sau goma.

A don haka suka fito zanga-zangar don nuna rashin jin daɗinsu da salon kamun ludayin Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, duba da yadda yake neman kassara rayuwarsu.

A ƙarshe, sun yi fatan dukkan masu ruwa da tsaki da su yi dukkan abubuwan da ya kamata, domin kawo wa talakawan Nijeriya ɗauki daga wannan hali da suke ciki.

By Editor