Yadda ake tunkarar tsadar rayuwa a Nijeriya

Spread the love

*Kotu ta tsoma baki
*Bankin CBN ya yi bayani
*Jiga-jigan gwamnati sun rufe ƙofa
*Shin zanga-zanga mafita ce?

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Matsalar tsadar rayuwa ta zama babban abinda a yau a Nijeriya aka fi tattaunawa a kai, saboda yadda farashin kayayyaki ke tashin gwauron zabo a kullum, yayin da talakawan ƙasar ke faɗi-tashin ganin sun tsira daga yanayin sakamakon yadda ƙarancin abin hannu ke cigaba da ta’azzara.

A ɗaya ɓangaren kuwa, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta na iƙirarin cewa, lallai ta na yin iyaka ƙoƙarinta wajen ganin ta shawo kan lamarin, wanda masana da masu nazari da dama ke kallo a matsayin ta gaji matsalar ne daga gwamnatin baya a ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Baya ga nuna damuwa a ɓangarori da sassa daban-daban na ƙasar da a ke yi, tsadar rayuwa ta kai ga an fara samun zanga-zanga da jerin gwano a wasu gurare a Nijeriya, don nuna wa gwamnati damuwa kan halin da ’yan ƙasa ke ciki, yayin a nata ɓangaren kuma, ita ma gwamnati ke ɗaukar wasu matakai na daidaita al’amura, kamar bayar da umarnin fitar da Dala daga asusun Babban Bankin Nijeriya (CBN) da bankunan kasuwanci, don daƙile tashinta a kasuwar shunku, fitar da abinci daga rumbun ƙasa, raba wa gwamnonin jihohi kuɗaɗen tallafi, don bai wa marasa ƙarfi, bayar da umarnin hana cinikayyar kaya da kuɗaɗen ƙasashen waje a cikin ƙasa da sauran matakai daban-daban.

Bisa la’akari da halin da a ke ciki ne, Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya yi kira ga al’ummar Nijeriya da su ƙara haƙuri da gwamnati, domin gyaran targaɗe sai an yi haƙuri, ya na mai cewa, ya yi wuri ’yan Nijeriya su yanke ƙauna kan gwamnatin Shugaba Tinubu, domin ta na nan ta na yin aiki tuƙuru, don ganin ta shawo kan wannan matsala, inda ya ƙara da cewa, amma hakan ba zai yiwu a rana ɗaya ba.

Zanga-zanga ta ɓarke a Suleja da Kogi kan hauhawar farashin kaya:

Wata sabuwar zanga-zanga ta sake varkewa a garin Suleja cibiyar kasuwanci ta jihar Neja mai tazarar kilomita kaxɗan da babban birnin tarayya, Abuja.

Hakan dai na zuwa ne a yayin da wasu ’yan Nijeriya galibi mata a jihar Kogi suka fito kan tituna domin nuna rashin amincewarsu da tavarvarewar tattalin arzikin ƙasar.

Masu zanga-zangar sun nuna rashin jin daɗinsu a ranar Laraba tare da yin kira ga gwamnatin da shugaban aasa Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta da ta magance matsalar tsadar kayayyaki da suke fama da ita.

Hotunan jerin gwanon dai sun ɗauki hankali a yayin zanga-zangar da ake ci gaba da yi, inda ‘yan ƙasar ke neman a ɗauki matakin gaggawa don rage musu raɗaɗin tattalin arziki.

Wani ganau ya ruwaito cewa, “Akwai wata zanga-zanga da a ke yi a yankin Ƙaramar Hukumar Suleja ta jihar Neja. Suna kira ga Tinubu da ya kawo ƙarshen wahalhalun da talakawa ke fama da shi a kullum a ƙasar nan.”

Hakazalika, mata da maza ‘yan kasuwa da suka gudanar da zanga-zanga a titunan Lokoja, babban birnin jihar, sun koka da yadda farashin kayayyakin masarufi ke ƙaruwa da kuma yadda hakan ya shafi sana’o’insu.

’Yan kasuwan sun rufe shagunansu saboda sun daina samun tallafi saboda tsadar kayayyaki.

Wata daga cikin masu zanga-zangar, Misis Ladi da ke sana’ar shinkafa da wake, ta ce ƙaruwar farashin kayan masarufi ya shafi kasuwancinta ne saboda ta ci gaba da samun raguwar masu cin abinci.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka gudanar da irin wannan zanga-zanga a Minna, babban birnin jihar Neja, inda ɗaruruwan mutane maza da mata da matasa suka bayyana kokensu dangane da hauhawar farashin kayayyaki.

Mata a kasuwar Ogun sun bayyana vacin ransu kan tsadar rayuwa:

Wasu matan kasuwa a jihar Ogun sun yi barazanar doke shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu idan suka yi ido biyu da shi yayin da matsalar tsadar rayuwa ke ƙara ƙamari.

Matan sun bayyana ɓacin ransu da halin ƙuncin da ake ciki na tattalin arziki, sun bayyana damuwarsu ne a wata ganawa da manema labarau a ranar Laraba.

Sun yi nuni da cewa Tinubu ya kunyata ’yan Nijeriya, musamman Yarbawa.

Wata dattijuwa ta ce “Ya vata mana rai a ƙasar Yarbawa, ba ya hali irin na Yarbawa.”

Wani kuma ya ce “Komai yana da tsada ta yadda ba za mu iya sayen garri kwano ɗaya ba. Mun gaji da komai, lokacin da na fara kasuwanci, kwalin kifi naira 200 ne amma yanzu ya kai naira 20,000.

Farashin kananzir ya kere na fetur da gas zuwa Naira 1,362 a lita ɗaya:

Talakawa na iya fuskantar wahalhalu yayin da farashin kananzir ya kai Naira 1,362 a kowace lita, inda ya zarce na man fetur da dizal.

A ranar Laraba, bayanan Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) sun nuna ƙaruwar kashi 5.8% idan aka kwatanta da Naira 1,287 da aka samu a watan Nuwamba 2023.

Dangane da bayanan NBS, a cikin Disamba 2023, matsakaicin farashin man fetur ya kai N672, dizal ya kasance N1,227, amma gas musamman a Jigawa, farashinsa ya kai kusan Naira 1,145 akan kowace KG.

Binciken kowace shekara ya nuna ƙaruwar kashi 23% a matsakaicin farashin kananzir a kowace lita, wanda ya tashi daga N1,105 a watan Disamba 2022.

Bayanin ya nuna cewa Abuja ta samu mafi girman farashin kowace lita a kan N1,650, sai Ogun a kan N1,610, Benuwai kuma a kan N1,594.

Kotu ta umarci Tinubu ya ƙayyade farashin kaya cikin mako guda:

Wata babbar kotun tarayya da ke zama da ke Ikoyi a Jihar Legas a ranar Laraba, 7 ga Fabrairu, 2024, ta umarci Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta ƙayyade hauhawar farashin kayayyaki da na man fetur cikin kwanaki bakwai.

Mai Shari’a Ambose Lewis-Allagoa ne ya bayar da umarnin a ci gaba da gabatar da buƙatar da mai ƙara kuma ɗan rajin kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana SAN ya gabatar.

Alƙalin kotun ya umurci Gwamnatin Nijeriya da ta ƙayyade farashin Madara, Gari, Gishiri, Sukari, ashana, kaɗaɗen baburan hawa da kayan gyaransa, motoci da kayayyakin gyara da kuma kayayyakin man fetur, waɗanda suka haɗa da: dizal da kananzir.

A cewar Alƙalin, “Na ji mai ƙarar Femi Falana a cikin ƙararsa mai lamba FHC/L/CS/869/2023 kuma na gano duk da ƙarar da aka shigar kan masu kare kansu, Atoni-Janar da Hukumar Kula da Farashi babu wata hammaya da aka samu dangane da haka, wanda haka doka ce cewa an amince da dukkan hujjojin da aka gabatar.”

“Kotu ta gano cewa waɗanda ake ƙarar ba su mayar da martani kan wannan ƙarar ba duk da cewa an aika masu da takardar ƙarar.”

Alƙalin kotun ya ci gaba da cewa, “Don haka ne wannan kotun, ta karɓi dukkanin roƙon da mai shigar da ƙarar ya gabatar gaban kotun.

“Kotu na umurtar gwamnatin Nijeriya ta ƙayyade farashin madara, fulawa, sukari, gishiri, kekuna, ashana, babura, motoci da kayayyakin gyaransu.”

Fita karatu ƙasashen waje da yawon shaƙatawa ke karya darajar Naira – CBN:

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, CBN, Olayemi Cardoso ya bayyana cewa, abubuwa kamar fita karatu ƙasashen waje, fita neman lafiya da yawon shaƙatawa ke ƙara karya darajar Naira.

A ranar Talata ne Majalisar Wakilai ta gayyaci wasu manyan jiga-jigan jihohin ƙasar kan halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki, inda a ƙarshe ’yan Nijeriya suka samu tabbacin cewa nan ba da daɗewa ba abubuwa za su daidaita.

A muhawarar manufofin ɓangarori don magance tsadar rayuwa akwai; Ministan Kuɗi kuma Ministan Tattalin Arziki Wale Edun, Ministan Kasafi da Tsare-tsare na Ƙasa Atiku Bagudu, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) Yemi Cardoso, da Shugaban Hukumar Haraji ta Ƙasa (FIRS) Zacch Adedeji.

An kuma bayyana yadda ‘yan Nijeriya suka kashe sama da dala biliyan 40 don samun ilimi da kiwon lafiya a ƙasashen waje tsakanin shekarar 2010 zuwa 2020, da kuma dala biliyan 58.7 da gwamnati ta kashe kan kuɗaɗen tafiye-tafiye na sirri a daidai wannan lokacin.

Da yake jawabi, Gwamnan CBN Cardoso ya ce, “akwai damuwa dangane da tsadar rayuwa a Nijeriya, kuma muna aiki tuƙuru don samar da mafita mai ɗorewa”. Ana sa ran hauhawar farashin kayayyaki zai ragu a shekarar 2024.

Da yake bin diddigin ƙalubalen kasafin kuɗi na yanzu, ya ce ’yan Nijeriya sun kashe sama da dala biliyan 40 don samun ilimi da kiwon lafiya a ƙasashen waje tsakanin 2010 zuwa 2020, adadin da Cardoso ya ce, ya zarce asusun ajiyar waje na ƙasar a halin yanzu.

A cewarsa, yawan ’yan Nijeriya a makarantun ƙasashen waje da yawon buɗe ido na daga cikin manyan abubuwan da ke jefa Naira cikin matsin lamba.

Ya ce buaatar dala da waɗannan ɗalibai da masu fita aikin likita a ƙsashen waje ke yi na yin illa ga Naira, inda ya ce adadin ɗaliban Nijeriya da ke karatu a wajen ƙasar ya ƙaru matuƙa, kuma an kiyasta sun haura ɗalibai 100,000.

Jiga-jigan Gwamnatin Tarayya sun yi ganawar sirri kan tsadar rayuwa:

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila ya yi ganawa ta sirri da mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu da wasu ministoci a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Taron wanda aka fara da misalin ƙarfe 05:30 na yamma kuma ya samu halartar ministocin ilimi, Dr Tahir Mamman; Kuɗi, Wale Edun; Noma, Abubakar Kyari da kuma ƙaramin ministan Noma, Mustapha Shehuri.

Duk da cewa har yanzu ba a bayyana ajandar taron ba, an ce bai rasa nasaba da batun samar da abinci ba, musamman tashin farashin kayan masarufi da ke haddasa tarzoma a wasu jihohin.

An kuma tattaro cewa taron na kwamitin shugaban ƙasa kan bada agajin gaggawa na abinci, wanda shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa ya kira.


Taron dai na zuwa ne biyo bayan zanga-zangar da mata suka yi a garin Minna na jihar Neja da na wasu fusatattun matasa a Kano kan tsadar rayuwa a ƙasar.

Sai dai kuma duk da matakan da gwamnati ke cewa, ta na ɗauka, hakan bai hana talakawan ƙasa cigaba da zafafa damuwa kan halin ƙunci da su ke ciki ba ta hanyar nuna aniyar fitowa zanga-zanga, wacce wasu masu nazari ke nuni da hatsarin hakan, domin wasu na iya amfani da wannan dama wajen tayar da tarzoma.

Amma daga nazari da binciken da Blueprint Manhaja ta yi, lallai akwai buqatar gwamnati ta ɗauki matakin gaggauwa, domin ’yan Nijeriya sun gaji da gafara sa irin wacce su ke ganin gwamnatin baya ta riƙa yi mu su ba gare da sun ga alamun ƙaho ba.

By Editor