Daga BASHIR ISAH
Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin Nijeriya sun cimma wannan matsaya ne a wata ganawa da suka yi ranar Alhamis.
Ministan Labarai da Wayar da Kan ‘Yan Ƙasa, Mohammed Idris ne ya shaida wa manema labarai hakan a Fadar Shugaban Ƙasa jim kaɗan bayan kammala taron gaggawar da Shugaba Tinubu ya shirya.
Idris ya ce za yi tarurruka da daman gaske a kan yadda zs a tsara da kuma samar da ‘yan sandan jihar a Nijeriya .
A cewarsa, “Amma a yanzu ana kan tattauna batun ‘yan sandan jiha. Gwamnatin Tarayya da ta jihohi suna tattauna yiwuwar samar da ‘yan sandan na jiha.
“Tabbas za a yi tattaunawa mai zurfi kan batun, akwai aiki mai yawa da za a yi don cimma hakan. Amma Gwamnatin Tarayya da jihohi sun amince kan cewa akwai buƙatar hakan.
“Wannan cigaba ne mai amfani. Amma kamar yadda na faɗa ne cewa, akwai aiki mai kafin cimma haka. Za a yi tarurruka masu yawa a tsakanin sassan gwamnati domin shirya yadda haƙar za ta cimma ruwa,” in ji Idris.
