Daga BASHIR ISAH
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) reshen Jihar Neja ta sanar da janye yajin aikin da ta fara a ranar Laraba a jihar.
Ƙungiyar ta ce ta dakatar da yajin aikin ne biyo bayan yarjejeniyar da ta suka cimma da ɓangaren gwamnati da kuma don bada zarafin ci gaba da tattaunawa a tsakanin ɓangarorin biyu.
Shugaban NLC a jihar, Abdulkareem Lafene, shi ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan tattaunawar da suka yi da ɓangaren gwamnati a ranar Laraba.
Haka shi ma Gwamnan Jihar, Mohammed Umaru Bago, ya ce lallai sun cimma yarjejeniya kan gwamnatin jihar za ta magance buƙatun da suka ingiza ƙungiyar shiga yajin aiki a jihar.
Bago ya ƙara da cewa, galibin matsalolin da NLC ke ƙoragi a kai ya gada ne daga gwamnatin da ta gabata.
Ya ce an kafa kwamiti na musamman mai ɗauke da mambobi daga ɓangarori daban-daban na gwamnati wanda zai yi nazari kan wasu dokoki da suka shafi buƙatun na NLC.
Shugaban Ma’aikata na Jihar, Salisu Abubakar da Babban Sakataren Ma’aikatar Kula da Harkokin Ƙananan Hukumomi da Masarautu, Abubakar Aliyu, su ne suka jagoranci ɓangaren gwamnati wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar.
Sannan Abdulkareem Idirs Lafene na NLC da Ibrahim Gana na TUC, sakataren JPSNC, Anna Simon, Shugaban JAC na Jiha, Aminu Mahmud, su ne suka wakilci NLC wajen sanya hannu a yarjejeniyar.
