Duk waƙar da ta rubutu, babu wanda ba ya iya rera ta – Malumman Matazu

“Jigon waƙa na cikin ababen da ke ban wahala”

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS

A satin da ya gabata, shafin Adabi ya samu baƙuncin ƙwararre a ɓangaren rubutacciyar waƙa, Abdulhamid Muh’d Sani Matazu, inda muka faro tattaunawar kan abinda ya shafi ma’anar rubutacciyar waƙa da abinda ya bambanta ta da waƙar baka. Kafin mu kai ga tasirin da shawarwarin da suke bayarwa a waƙe suke yi.

A wannan makon za mu ɗora ne daga inda muka tsaya:

MANHAJA: Me yafi baka wahala a yayin rubuta waƙa?

MALUMMAN MATAZU: Jigo ko dalilin waƙa na cikin abin da ke ban wahala, a cikin al’amarin rubuta waƙa, irin waƙoƙinmu kashi 95 cikin 100 waƙoƙi ne na gaskiya da gaskiya, duk abin da za mu yi wa waqa, zahiran abin akwai shi, ba waƙa ce ta neman abin duniya ba, kuma yawancinmu muna ƙyamatar mu rubuta abin da ba gaskiya ba, don haka duk lokacin da aka ce mui waƙa kan wani abu da ba haka abin yake ba, to waƙar ma sai ta gagara.

Abu na biyu tushen waƙa wato amshin waƙar shi ne abu mafi wahala ga waƙa, in sha’iri ya samar da amshin waƙa, to ya samar da babban kaso cikin waƙar da ya nufaci rubutawa. Ƙari a kan haka ita waƙa baiwa ce ta Allah, da yawan lokaci ƙwararren sha’iri ma yakan ɗauki takarda da alƙalami ya kuma keve da niyyar rubutata, amma sai Allah ya riƙe abin sa.

Ta yiwu kuma bayan tashinsa daga wurin, wataƙila ma yana wata hidimar sai kuma Allah ya kawo ta, don haka in dai sha’iri ya kai sha’iri to da wahala ka gan shi babu takarda da alƙalamin rubutu a tattare da shi, in kau ya rasa wannan to yana tare da wayarsa da ta zo sai ka ga yana ta ƙoƙarin ya rubuta, don in bai rubuta ba za ya iya nemanta kuma ya rasa. Ina ƙara nanatawa waƙa fa ikon Allah ce.

Wane kira gare ka ga sababbi da masu burin fara rubuta waƙoƙi?

Babu shakka rubuta abu kamar furta shi ne a baki, don haka marubuta bakiɗaya ma, ba marubutan waƙoƙi kaɗai ba, suna cikin babban ƙalubale na abubuwan da suke rubutawa, wani ƙalubalen tun a nan duniya za su fara fuskantar shi, kira na gare mu, mui takatsantsan ainun kan duk abin da zamu rubuta, babu shakka akwai ranar da Allah zai tambaye mu kan aikinmu.

Duk abin da zamu rubuta mu rubuta wanda zai amfane mu a duniyarmu da lahirarmu, mu ƙaurace rubutun da zai kawo rarrabuwar al’umma, tare da duk abin da zai kawo tasgaro ga al’ummarmu addininmu da makamantan hakan. Bayan wannan ya zamar ma dukkan nau’o’in marubuta na zube ko na waƙoƙin kai kowanne irin nau’in rubutu ma, da su nemi ilmin rubutun daga masana harkar ta rubutu.

Zuwa yanzu da yawan waɗanda ke bibiyar rubutattun waƙoƙin Hausa da ake rubutawa a wannan lokaci zai wahala a ce bai san rawar da ka ke takawa a ɓangaren ba. Shin ko akwai wani shiri da wani ko wasu ko kai kanka ke yi, na tattara waɗannan waƙoƙi zuwa kammalallen littafin waƙoƙinka?

Na’am! A lokacin da na fara fafutikar fitar da diwanin waƙoƙin nawa, sai Allah ya sa na samu gurbin karatun digiri a jami’a, harkar karatun sai ta ɗauke man duk hankalina ga aikin.

Allah da ikonsa gab da kammala karatun kuma sai wata jami’a ta gayyace ni taronsu na makon Hausa, zuwana na gabatar da waƙata mai suna ‘Gagara Gwari’, waƙar waƙa ce da ke yin cikakken bayani a kan muhimmancin harshen Hausa, ƙari a kan haka waƙar tana da sarqe-sarƙen harshen namu na Hausa, tare da kalmomin harshen masu wahala, babu shakka wannan waƙa da na rera a wurin ta fa’idantar matuƙa ga mahalarta wannan taro.

Bayan dawowata gida sai wasu cikin ɗaliban jami’ar suka yi ta tuntuɓata kan wannan waƙa, da ma sauran wasu waƙoƙin da na rubuta, suna so in ba su waƙar don nazari da adanawa, ashe bayan ni ma ɗaliban sun riqa samun wasu cikin malamansu don sashen ya taimaka musu, ya samar musu da wasu cikin waƙoƙin da na wallafa, ilai kuwa ashe su ma cikin malaman nasu tuni sun fara tattauna yadda za su neme ni don tabbatuwar tattara waƙoƙin zuwa littafi.

Ya zuwa yanzu dai tsare-tsare sun yi nisa da aikin tattarawar, domin kuwa malaman jami’ar har guda uku ne ke aikin, kuma zuwa yanzu an samu tattara waƙoƙi fiye da ɗari, kan jigo mabambanta, har ma sun saka ma littafin suna, nan gaba gab da fitar littafin zan sanar da sunan, da sauran ma wasu abubuwan da ya ƙunsa insha Allah.

Aikin littafin aiki ne da ake yi cikin tsanaki don suna son aikin ya zama ingantacce kuma karɓaɓɓe ga al’umma in sha Allah.

Fatan da nake tare da addu’ata kullum shi ne aikin ya kammala ina raye, kuma a kurkusa insha Allah, ina ɗaukar cewa fitar littafin nan ina raye babbar nasara ce, a aikin adabi na.

A matsayinka na masani kan waƙa. Za mu so ka yi wa masu karatu gamsashen bayani kan ƙa’idojin rubuta rubutacciyar waƙa?

Haƙiƙa rubutacciyar waƙa ta bambanta da maganar yau da kullum da ɗan’adam ya ke furtawa, duk da cewa ita ma maganar ce, to amma ita tana da wasu ado da suka baibaye ta don haka ta bambanta ɗin da magana ta baki. daga cikin waɗannan abubuwa da suka bambanta waƙa da sauran magana ga wasu daga ciki tare da ɗan misali. kamar yadda masana abin suke naƙaltowa :

  1. Ɗango : Abin da ake ce ma ƙango shi ne: layi ko sheɗara na zubin waƙar. Misali waƙa mai sheɗara ɗaiɗai, bibiyu, uku-uku, hurhuɗu, ko biyar-biyar, wasu masanan suka ce za ta iya wuce biyar-biyar ɗin ma, sai dai wasu masanan sun ce duk waƙar da ta wuce ɗango biyar ba ta amsa sunan rubutacciyar waƙar ba.

Ga wasu misalai daga wasu waƙoƙi, mu fara da waƙar ‘Muhimmancin Takalmi’ da na rubuta:

“Takalmi ni ban raina shi,
Sam-sam ban son mai kushe shi,
Dalili don amfanin shi,
Bani ganin tsadar takalmi.

Budurwa duk ƙwalisarta,
Matar aure duk matsayinta,
Diresin ko ta ƙure ta,
Wajibinta ta sa takalmi.

Duk sheɗara ɗayar da nai wa waqafi, ita ake kira da ɗango. Ni kuwa a ra’ayina in dai waƙa tana da ƙafiya, ma’auninta ya daidaita da sauran ƙa’idojin da aka tanada, ko ta kai ɗango nawa to sunanta rubutacciyar waqa. Ni kaina ina da irin waɗannan waƙoƙin masu ɗangaye da yawa, akwai waƙar ‘Alƙur’ani’ da kuma wata da nai ma wani aminina kuma marubuci Malam Bello Hamisu Ida.

  1. Amsa amo/Ƙafiya: A harshen mu na Hausa ana ce wa Amsa-amo amma da harshen Larabci ana ce mata ƙafiya. To menene Amsa-amo/ƙafiya? Ma’anarsa shi ne samuwar harafi iri ɗaya wanda kowane baiti ko ɗango zai riqa ƙarewa da shi, ƙafiya ta kasu kashi biyu, akwai ƙafiyar ciki, akwai kuma ƙafiyar waje ga misali daga waƙata ta Gagara-gwari:

“Ƙaƙƙarfan ƙato mai maiƙo,
Sarƙa sassauƙa ga saƙo,
Saƙon maiƙo ne, to miƙo,
Duk don amfanin ‘yan Hausa.

Kalmomin miƙo, saƙo, maiƙo, da suka zo a wannan baitin duk ƙafiya ce amma ta ciki, sai dai kalmar Hausa da ta zo a ƙarshen baitin ita ce ƙafiyar waje.

  1. Zaɓen kalmomi: Zaɓen kalmomi abu ne da aka fi so sha’iri ya ƙoƙarta wajen yin sa a lokacin da yake rubutun waƙarsa, zaɓen kalmomin da suka dace abu ne mai kyau ga rubutacciyar waƙa, kuma shi ne ke sa waƙar ta zama ingantacciya.
  2. Awon waƙa: Abu ne da ya zama wajibi ga marubucin waƙa ya zama waƙarsa tana zama awonta ya daidaita, ya zama in ma akwai fin bai taka kara ya karya ba, ga misalin baiti uku daga waƙar ‘Muhimmancin Rubutu’ da na rubuta:

A. Komai in za ka rubuta,
Ƙalƙalce shi iya buƙata,
Sannan duk hujja riqe ta,
Hujjar ce madogararmu.

B. Marubuci kar kaj ji tsoro,
Don aikinmu hani da horo,
Alhaji har mai tura baro,
Duk ɗaya ne mu ag gare mu.

C. Rubutu in da gaskiyarka,
Kar ka ji tsoron dukka hauka,
Rabbu yana nan wanda yai ka,
Zai kare ka ga dukka gumu.

In muka lura da jerin waɗannan baitukan zamu ga cewa yanayin yawan kalmomi da haruffansu duk kusan ɗaya ne, idan ma akwai fi to fin bai taka kara ya karya ba, misalin haka ake so rubutacciyar waƙar Hausa ta kasance.

Ga ƙarin misalin baiti biyu daga waƙar “Ɗanyen Hukunci” da ita ma ni na rubutata:

” In mun haɗu wasu na ƙifce,
Ban ce ba sai a ce na ce,
Ku ci bashi kan biyan rance,
Fatan da nake nayo dace,
Sanadin sharrin da nammima.
Sharrin har ƙage sun min ni,
Su dai son su su jefa ni,
Cikin tsanani da ruɗani,
Na daure na ƙi wayyoni !!!
Guduna tada tarzoma.

  1. Rerawa: Rera rubutacciyar waƙa na cikin magi da gishirin rubutacciyar waƙa, Malam Nasiru G. Ahmad Kano ya tava faɗa man cewa duk waƙar da ta rubutu, to babu wanda baya iya rerata, domin kuwa idan waƙa ta rubutu da ka fara karantata ma sai ka ji lafiya lau kamar ma rerawar ka ke yi, zan so mai karatu ya koma, ya ƙara karanta waƙar can da na rubuta ta ‘Marubuta’, wataƙila ya ƙara amincewa da abin da na faɗa.
  2. Jigo: Jigo shi ne saƙon da aka gina tubalin waƙar a kansa, ma’ana saƙon da ake son isar wa a waƙar da aka yi nufin rubutawa. Bari in bada misali na jigon waƙar ‘Kowa Ya Tuna Bara…’ wadda nai kan matsalar tsaro da Arewa ke ciki, da har Jami’ar Usman Ɗanfodiyo ta Sakkwato ta karrama mu a kan ta, ga baitin:

“Waƙar kan halin Arewa,
Da muke yau na firgitarwa,
Zan mana ne don Faɗakarwa,
Da shawara zan har nusarwa,
Fatana Allah ya yaye.

A wannan baitin ƙwara ɗaya na faɗi duk abin da na hakaito a waqar mai baituka (49). Wannan a taƙaice shi ne ake ce wa jigon waƙa.

Bayan wannan ma ga wani jigon waƙar daga waƙata mai suna: ‘Cikakkar Nasaba’ wadda na rubuta ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW) ga jigon :

Waƙa na shirya yau za ni yo Sha-kundum,
Gun Annabinmu Shumagaban ‘Yan’Alam,
Babbar dabara riqe Muhammadu gam-gam,
Mai ƙin Rasulu mu bar biye mishi sam-sam,
In mun bi Manzo mun ƙaurace ga halakka.

Duk da cewa wannan waƙa tana da baituka goma sha biyar (15) amma na taƙaita jigon waƙar a baiti guda.

Wannan shi ne bayani a taƙaice a kan jigon waƙa.

Waɗannan misalan da makamantansu, su ne taƙaitaccen bayani a kan rubutacciyar waqa, kamar yadda malaman abin suka nunar. Duk wannan bayanin ɗan taƙaitacce ne na yi, sai dai zai iya zama jagora, ga duk mai son sanin wani abu a ilimin rubutacciyar waƙar Hausa.

Ba zai yiwu ace ɗan’adam kan harkarsa nasarori kaɗai ya samu, bai samu ƙalubale ba. Shin waɗanne irin ƙalubale ka fuskanta a rubutun waƙoƙi da ma sauran rubuce-rububucenka?

A harkar rubutun nan na kamar sauran marubuta ‘yan uwana, ni ma na haɗu da ƙalubale daga wasu ‘yan uwa da abokan aiki, wasu lokuta sukan faɗi man maganar da ban jin daɗi, misali ga ɗaya daga cikin irin maganganun:

”Me za ka rubuta yanzu, wanda ba ai mafiyin sa ba a baya?, kana ɓatawa kanka lokaci ne kawai kan rubuce-rubucen nan da kake yi.”

Wannan wata ce cikin maganganun da ake faɗa man, kan harkar nan ta rubutu, a wasu lokuttan kamar gwiwata tai sanyi sai dai ma kawai na ji na ƙara ƙaimi ga aikin da na riga na san ni ne na sanya kaina, kuma na san abin bai saɓawa addinina ba, don hakan sai na cigaba da aikina cikin kuzari.

Wani babban ƙalubalen da na fuskanta kuma akan rubutun zube ne ba ma waƙa ba, kan wani fin ƙarfi da aka nunawa wasu ba’adi na jama’a, a shekarar 2015 a ɗaya daga cikin manyan biranenmu na Arewa, abu ne da ya raba kan al’ummar yankin gida biyu, (Ma’ana mutanen da ba su cikin waɗanda nake ganin an zalunta, da kuma waɗanda nake ganin su ne suka yi zaluncin) tsakanin waɗanda ni nake ganin masu tausayi ne, da waɗanda nake ganin rashin tausayinsu, kan al’amarin. Alhamdulillah ni sai na zamar cikin masu tausayawa ga waɗanda aka zalunta.

Tausayina ga mutanen da aka zalunta, ya ƙi ɓoyuwa a cikin zuciyata, hakan yasa na ɗauki wayata, na tafi farfajiyata ta kafar sada zumunta da mahawara (Facebook) in da na faɗi matsayata tare da Allah wadai, ga abin da akai wa wannan al’umma, da yawan mutanen da suka ga rubutun nawa, sun jinjina man, tare da yabawa ga gaskiyar da suka ce na rubuta. Sai dai tun lokacin da rubutun bai jima ba wasu suka ce nai shirin tunkarar ƙalubale.

A in da nake wasu ba’adin al’ummar da nake tare da su, ba su ji daɗin rubutun nawa ba, sai ma suka sanya man qahon zuqa, matakin farko da suka fara ɗauka kaina shi ne korata aiki da suka yi daga makarantunsu, tare da cinno min da jami’an tsaro, in da suka gayyatan ofishinsu don yin zama da ni, daga baya dai jami’an sun fahimci tuhume-tuhumen da al’ummar can sukai man duk makirci ne da ƙiyayya.

Hakan ya sa na fita sha’anin jama’ar da sukai man makircin na cigaba da hidimata. Babu shakka wannan al’amari ya zamar man babban ƙalubale da tarihin adabina ba ya cika ba tare da na kawo shi ba.