*Ya ce an haramta kai wa ‘yan ta’adda biredi a jihar
Daga BASHIR ISAH
Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya yi ƙarin haske inda ya ce bai haramta samar da biredi a sassan jihar ba.
Sai dai, ya ce ya haramta duk wata hanya da ake amfani da ita wajen taimaka wa ‘yan fashin daji da biredi a jihar.
Dauda ya yi wannan ƙarin hasken ne biyo bayan dakatar da samar da biredi a jihar da Ƙungiyar Masu Gasa Biredi ta yi a sakamakon dakatar da harkar babura masu kai wa ‘yan fashin daji biredi a jihar da gwamnati ta yi.
Sanarwa da aka fitar ranar Laraba a Gusau mai ɗauke da sa hannun Kakakin gwamna, ta nuna gwamnati ta ɗauki wannan mataki ne domin yaƙi da hanyar da ake bi wajen taimaka wa ‘yan bindiga da kayan masarufi a jihar.
A cewar sanarwar, “Gwamnatin Jihar Zamfara za tana so ta yi ƙarin haske kan labarin da aka yaɗa na cewa an hana masu gasa biredi ci gaba da harkokinsu a jihar.
“Gwamnati na mai tabbatar da cewa wannan ba gaskiya ba ne, kuma labarin ya haifar da ruɗani a tsakanin masu sana’a da ma al’umma baki ɗaya.
“Gwamnatin Zamfara ba ta da niyyar shiga lamarin sana’ar samawar da kuma sayar da biredi wanda shi ne abincin da ake amfani da shi a gidaje da dama.
“Muna jaddada cewa gwamnatinmu mai ƙarfafa wa sana’o’in cikin gida ne tare kuma da tabbatar da cewa jama’a na samun abinci na isa gare su.
“Muna sane da irin rawar da ƙananan sana’o’i ke takawa a tattalin arzikin jiharmu, sannan muna ƙoƙarin ganin an samar musu da kyakkyawan yanayi domin ba su damar gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali.
“Mun samar da tsari domin yaƙi da ‘yan ta’addan da ke haifar da tashin-tashina a wasu sassan jihar wanda ya haɗa da haramta kai musu biredi da fetur kasancewar sai da samun waɗannan kayayyaki za su iya samun halin ci gaba da harkokin ta’addancinsu.
“Gwamnatin Zamfara na fata ta dalilin aiwatar da wannan tsarin, za a iya maido da zaman lumana da tsaro a yankunan da lamarin ya shafa don ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Haramcin ɓangare ne na ƙoƙarin cimma wannan manufa.”
