‘Yan bindiga sun kashe fararen hula takwas a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Aƙalla fararen hula takwas ne ‘yan bindiga suka kashe a Ƙaramar Hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

Wani mazaunin yankin mai suna Muhammad Yusuf ya shaida wa Blueprint Manhaja ta wayar tarho cewa ‘yan bindigar sun far wa waɗanda lamarin ya rutsa da su ne a lokacin da suke aikin share hanya inda suka kashe takwas daga cikinsu.

A cewarsa, an kai harin ne a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 12:00 na dare.

Ya kuma bayyana cewa, a wannan rana mai albarka, an gano gawarwaki uku tare da binne su kamar yadda haƙƙin addinin Musulunci ya tanada a garin Maradun hedikwatar ƙaramar hukumar Maradun ta jihar yayin da sauran biyar ɗin kuma aka ƙwato su a ranar Litinin.

“Da jin labarin harin, mun matsa zuwa wurin inda muka kwashe mutane uku da suka rasa rayukansu a jiya Lahadi kuma a yau Litinin 19 ga watan Fabrairu mun sake qwato qarin mutane biyar kuma tun daga nan aka binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada,” ya ce.

Ya bayyana cewa mutane da dama sun jikkata yayin harin saboda akwai wasu mutanen da suka vata kuma ana ci gaba da neman inda suke.

“Kamar yadda nake magana da ku yanzu, muna neman wasu daga cikin mutanenmu da ba su koma gida ba bayan harin,” ya ƙara da cewa.

Muhammad ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta sake tura ƙarin sojoji zuwa jihar da nufin shawo kan matsalar rashin tsaro da jihar ke fama da ayyukan ‘yan bindiga.

“Mun lura da sake vullar ‘yan fashi a kusan ko’ina a jihar, muna kuma roƙon Bola Ahmed Tinubu da ya kawo mana ɗauki domin magance wannan ƙalubalen kafin abubuwa su ƙare a hannu,” ya ce.

Sai dai jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ASP Yazid Abubakar bai samu samun damar zuwa wurin haɗa rahoton da wakilinmu ya yi ba.

By Editor