Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Gwamnatin Jihar Zamfara ta biya Naira miliyan 613 ga ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya daga jihar su 414.
Shugaban kwamitin tantancewa kuma babban sakataren ma’aikatar kuɗi ta jihar Muhammad Kabiru Abubakar ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a ofishinsa.
A cewarsa, kwamitinsa ya karvi bayanai sama da 4000 na waxanda suka amfana.
Ya kuma kara da cewa an ɗora wa kwamitin ne domin tabbatar da waɗanda suka yi ritaya daga shekarar 2015 zuwa yau domin su ci gajiyar giratuti.
Ya yi alƙawarin yin adalci wajen sauke aikin da aka bai wa kwamitin nasa ta hanyar tabbatar da cewa an biya dukkan ma’aikatan gwamnati na gaskiya da suka yi ritaya.
“Muna aiki ba dare ba rana don kammala ƙoƙarin gwamnatin jihar na ganin duk ma’aikatan gwamnati na gaskiya da suka yi ritaya sun samu kyautarsu,” ya ce.
A cewarsa, atisayen zai duba waɗanda suke kan kuɗin fansa na ritaya, da kyautar kwangila da kuma kyautar mutuwa.
Ya kuma yi kira ga waɗanda suka amfana da su yi amfani da kuɗaɗensu yadda ya kamata domin ci gaban su da iyalansu.
“Muna kira ga waɗanda suka ci gajiyar tallafin da su tabbatar an yi amfani da kuɗaɗen da aka biya su yadda ya kamata domin kyautata rayuwarsu maimakon kashe kuɗaɗen da ba dole ba idan aka yi la’akari da taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar nan,” in ji shi.
