ECOWAS ta yanke shawarar ɗage wasu takunkuman da ta ƙaƙaba wa ƙasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da Guinea.
Ƙungiyar ta cimma wannan matsaya ne a wajen taronta da ta shirya ranar Asabar a Abuja.
Sai dai ɗage takunkumin ba na baki ɗaya ba ne, wasu ne daga cikin takunkuman da ECOWAS ɗin ta kafa wa ƙasashen da lamarin ya shafa.
Idan ba a manta ba, a watan Janairun da ya gabata Nijar da Mali da Burkina Faso suka sanar da ficewarsu daga ƙungiyar ECOWAS sakamakon takunkuman da aka kafa musu biyo bayan juyin mulkin da ya faru a ƙsashen.
