Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kotun hukunta laifukan yara da jima’i da kuma cin zarafin mata ta kai ƙarar wata lauya mai suna Adachukwu Okafor zuwa Sashen Kula da Masu Aikata Manyan Laifuka na jihar (SCID) da ke zama a babban kotun majistare da ke Awka a jihar Anambra.
An tsare wacce ake zargin ne a gidan yari bisa zargin yi wa mai aikinta mai shekaru 11 rauni a Onitsha.
Wacce ake zargin, mazaunin unguwar Chris Igwilo Street Akapka GRA, 3-3 Onitsha, an gurfanar da ita a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume biyu na aikata laifin da ta yi da gangan ga wani ƙaramin yaro (ɗan shekara 11), laifin da ake hukuntawa a ƙarƙashin sashe na 4(1) na dokar cin zarafin mutane (Hanawa da Kariya) na jihar Anambra ta Nijeriya 2017.
Sai dai wacce ake ƙara ta ƙi amsa laifin da ake tuhumarta da shi da kuma yi mata fassarar da ta gamsu.
A halin da ake ciki, buƙatar belin da lauyan wadda ake ƙara, Chijioke Nwankwo ya yi, kotu ta qi amincewa da shi, kuma an ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 28 ga Fabrairu, 2024, domin yanke hukunci.
Da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan zaman kotun, lauyan wanda ake ƙara, Chijioke Nwankwo ya zargi ma’aikatar mata da walwalar jama’a ta jihar da abin da ya kira “yin shari’a ta hanyar gwaji”, yana mai cewa hakan bai dace da shari’ar ba.
