An samu ƙaracin ruwan sha a Gusau Babban Birnin Jihar Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Al’ummar garin Gusau, Babban Birnin Jihar Zamfara na ci gaba da afkawa cikin yanayin matsalar ruwa sha tsawon makonni uku da suka gabata.

Binciken da wakilinmu ya gudanar ya nuna cewa wasu yankuna kamar yankin ‘reservation’ na gwamnati GRA, Gada Biyu, Birnin Ruwa, Tullukawa, Tudun Wada, Gada Baga, Kan-Wuri da dai sauransu na fama da matsalar ƙarancin ruwan sha ga rashin zubar da ruwan da ruwan jihar ya yi na makonni uku na ƙarshe.

Wakilinmu ya gano cewa yanzu haka lita 25 na ruwan da masu sayar da ruwan ke siyar da su kan Naira 100 maimakon Naira 50 .

Binciken da wannan kafar yaɗa labarai ta gudanar ya nuna cewa ana ganin yara da dama da sassafe a kullum suna neman ruwa a kowane lungu da saƙo tun farkon matsalar.

A zantawarsa da wakilinmu, mazaunin unguwar Hayin Malam Sani mai suna Malam Yunusa Garba, ya bayyana faruwar lamarin a matsayin mummunar varna.

A cewarsa, shida daga cikin ‘ya’yansa sun daina zuwa makaranta tsawon makonni biyu da suka gabata saboda ƙarancin ruwa a yankin.

“Ya’yana sun kasance suna fita kowace safiya don neman ruwa don buƙatunmu na yau da kullum amma ba za su dawo ba sai bayan 9:00 na safe don haka babu yadda za a yi su je makaranta duk tsawon wannan lokacin,” ya ce.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Zamfara da ta duba lamarin domin ganin an magance wannan ƙalubalen.

Sai dai wakilinmu ya ziyarci hukumar kula da ruwa ta jihar domin tabbatar da rahoton cewa ma’aikatan hukumar sun ƙi cewa komai saboda an ce manajan daraktan hukumar ya tafi Abuja ne domin ganawa da manema labarai.