Lawal ya ziyarci wuraren da ‘yan bindiga suka kai hari a Zurmi da Birnin Mgaji

*Ya sha alwashin kawo ƙarshen matsalar tsaro a Zamfara

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kai ziyara ƙauyukan da suka fuskanci harin ‘yan ta’adda domin ƙarfafa musu gwiwa game da sha’anin tsaro ƙarƙashin gwamnatinsa.

A makin davya gabata ne ‘yan fashin daji suka kai farmaki Nassarawan Zurmi da ke Zurmi da kuma Nasarawan Godel da ke yankin Ƙaramar Hukumar Birnin Magaji a jihar.

Kakakin Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar cewa, Dauda ya yi ziyarar ne domin nuna goyon baya ga al’ummar hare-haren suka shafa da kuma ta’aziyya ga ‘yan uwan waɗanda suka mutu a hare-haren.

Kazalika, sanarwar ta ce yayin da ya kai ziyara ofishin lyan sandan yankin da ‘yan bindigar suka ƙona a Nasarawan Zurmi, Gwamna Dauda Lawal ya tabbatar wa ‘yan sanda da cewa zai taimaka musu da kayan aiki domin ci gaba da ayyukansu yadda ya kamata.

“Ina mai alhini game da jami’ai biyun da suka rasa rayukansu yayin harin baya-bayan nan da ‘yan bindiga suka a Nasarawan Zurmi.

“Na fahimci irin damuwar da waɗanda lamarin ya shafa suka fuskanta, ina mai tabbatar muku cewa addu’o’i na tare da lyan uwan jami’an da suka rasa rayukansu da ma ƙauyen baki ɗaya.

“Na yaba da ƙoƙarin dakarunmu da yaƙe da ‘yan fashin dajin. Muna yaba da faɗi-tashin da kuke yi wajen bai ƙauyukanmu kariya yadda ya kamata.

“Gwamnatina za ta ci gaba da bai wa dakarun goyon bayan da suke buƙata. Za mu ci ƙarfin wannan matsalar muddin muka haɗa hannu.”

Bugu da ƙari, yayin ziyarsa Nasarawan Godal a Ƙaramar Hukumar Birnin Magaji, Gwamna Lawal ya bai wa al’ummar yankin tabbaci ya aika da kayayyakin tallafi biyo bayan harin. Tare da ƙarfafa musu gwiwa game da gwamnatinsa.