MAKAMASHI: Tallafi, manufa da buri bisa al’ada

Spread the love

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI

Kafofin yaɗa labarai, musamman jaridu da mujallu, su na da fili daga cikin filayensu da su ke kira da ‘record’, wanda wasu jaridun na harshen Hausa a gida Najeriya su ke kiran wannan fili da fayil, amma a jamhuriyar Nijar kuwa na fassara wannan fili da Dose duk dai da nufin cewa fili ne na a jiyar wani tarihi ga mutumin daya baiyana wannan batu ga karan kansa ko kuma ga ƙasar da yake ciki da ma duniya baki ɗaya.

Babban misali da yake cikin fayil-fayil na tarihin ƙasannan shine yadda Marigayi Malam Aminu Kano ya fassara wannan ƙasa ta Najeriya a matsayin ‘kasuwa’, inda kowa za shi yaci wannan kasuwa ta baje hajjarsa, amma idan yamma tayi kasuwa taci ta cinye, za’a koma gida a kirga riba ko faɗuwa. Akwai darusa masu tarin yawa daga bayane na ma’anar ƙasa kamar Najeriya a matsayin kasuwa inda har yake cewa, “kowa ya san gidan ubansa, da kasuwa ta tashi gidan ubansa zai nufa domin kirga sakamako”.

Kamar dai wannan batun cire tallafin man fetur da shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu yayi a ranar 29 ga Mayun shekara ta 2023, wanda a cikin jawabinsa na kama aiki a matsayin shugaban ƙasa, wanda a makon da ya gabata ya cika shekara guda cif-cif da cire wannan tallafi inda miliyoyin ‘yan ƙasa musamman talakawansu da wasu ‘yan takarda da suke ji a jikinsu daga cire wannan tallafi, har yake suna tambaya wai shin mene ne wannan tallafin? Kuma mene ne manufa da burin a bayar dashi? A bisa al’ada, da hikimar rayuwa, mene ne dalilin bayar da shi ga ‘yan ƙasa ko kuma akashin haka na cire shi kamar yadda gwamnatin Bola Ahmad Tinubu da Kashim Shatima Mustapha suka yi?

Masu sharhi a al’amuran yau da kullum da masana tattalin arziki da siyasar duniya musamman ma’abota damakaraɗiya, masu a guji siyasar garguzu da ta akidar addinai da suke da alaƙa da addinin Annabi Ibrahim (ASW), musamman addinin musulunci. Ƙasashen da suke da akidar damakaradiya, su suke zo da tallafi ga ‘yan ƙasa domin gujewa tirjiya da bore ga attajirai da shugabanni da ‘yan koransu, wato dai waɗanda ‘yan akidar gurguzu suke kira da ‘ɓarayin zaune’.

Kamar yadda muke faɗa a kullum a wannan shafi shine, siyasar mai kaza, idan aka zo rabo a bashi kan kaza da ƙafafu kuma a hana shi Magana, idan kuma yayi Magana a mayar masa cewa, kafin a dafa kazan nan sai da aka yi kayan miya da kayan ɗanɗano da gishiri da man miya da itacen wuta da tukwanan girki da murfu ya ɓata lokaci, uwa uba leburanci, wato ‘labour’ masu akidar damakaraɗiya suna amfani da wannan zarwance domin su kwashi dukiyar ƙasa su bawa ‘yan ƙasa fince su kuma su sha dabge.

Wannan ta sa wannan gwamnati ta Bola Ahmad Tinubu ta bujirewa ‘yan ƙalilan da basu kai kashi uku (3%) cikin ɗari ba suna karɓar naira tiriliyon goma sha biyar da biliyan dubu ɗari huɗu (15.4 trillion) su kai dai a duk shekara. Gwari-gwari, mutane da basu fi su hamsin ba (50) a Najeriya suna karɓar waɗannan kuɗaɗe a madadin ‘yan Najeriya sama da Miliyan ɗari biyu da ashirin (220M) da sunan tallafi, domin mu fahimta ‘Trillion’ guda ta fi yawan tan talatin (30T) na kwayar gero ko maiwa, inda zaka ɗauka kowacce ƙwaya a matsayin naira dubu. Idan aka baka buhu guda na gero, kowacce ƙwaya a matsayin naira dubu zai ɗauke ka shekaru nawa ka na kashewa?

Dukkan wahalhalu da ake sha daga lokacin da aka tsayar da wannan tallafi shine a matsayin ka mai kaza ko zabo, idan aka dafa wannan kaza ka karbi kai ko ƙafofi ka haƙura, saboda kai ɗan Bora ne, amma ‘ya’yan ‘yan mowa, suna wadaƙa da cinyoyi da fuka-fukai, wasu ma da ƙirji, wasu ambasu wuya da kayan ciki duk da cewa kazar kace. Babu adalci a wannan rabo, don haka muke tare da Bola Ahmad da Kashim Shatima.

Shawara itace, a daina bawa gwamnoni wannan kason kuɗaɗe, su baiyana buƙatun su a abubuwa da talaka zai amfana kai tsaye, a faggen noma da kiwo da hanyoyi a ƙananan hakumomi 774 da ake da su da samar da ɗakunan shan magani (clinics) da horar da waɗanda zasu ayyuka a wannan gurare. Da kuma mayar da hankali a ilimin piramare da ƙaramar sakandare. A tabbatar kowa zai iya karatu da rubutu da dukkan wasu alamu (symbol) da zasu taimake su a rayu ba. Tallafi buron-buron ne a duk wata ƙasa ta damakaraɗiya shi suke kira da ‘a kori kare daga gindin ɗinya’.

Ma’ana a basu dama su ci su yi teba shiyasa suke so a kori ‘kare’ wato sun kira mutum da kare domin su ƙanƙantar dashi, abinda bashi da daraja duk da cewa Allah ya ƙarramta mutum ta bas hi hankali da hangen nesa, wanda y aba shi dama yazo da fasaha da kimiyya har ta kai ka wata da shiga ƙarƙashin teku domin ebo dukiyar da Allah ya ajiye masa domin amfanin sa da su dabbobi har karan da suke Magana a kansu. Wannan tsari daga ni sai ‘ya’ya na, amma sauran maƙota da ‘yan lungu da ‘yan gari har uwa ‘yan ƙasa ko oho! Shi Bola Ahmad yace mun ƙi, don haka “no going back”.

Tsarin ba sani ba sabo a sha’anin noman damina dana rani na wannan gwamnatin shiri ne da ya zama wajibi ga gwamnatin nan ta Bola Ahmad Tinubu. Gwamnati ta fashi haƙan wajan wayar da kai da mutane su rungumi noma da kiwo. Duk wani abu na more rayuwa kai ga abinci ba, duk ƙasar da bata iya ciyar da kanta ta dauwama a matsayin baiwa. Itada ‘yanci har abada. Wannan daliline yasa muke kira ga ministan yaɗa labarai da wayar da kai cewa ga aiki ya same su.

Batun tsare-tsare da suka haɗa da faɗaɗa filayen gona zuwa hekta 500,000 shi ma wajibi ne ga dukkan gwamnoni ƙasar nan su bayar da hadin kais u taimaki ita gwamnatin ta taraiya na tabbatar an cimma wannan buri. Su ma jihohi da ƙanan hukumomi su rungumi wannan tsari ta yadda za’a kai gaci. Kuma muna kira ga ‘yan hamayya da su guji hana ruwa guda wajen wannan al’amara na noma da kiwo. ‘yan kasuwa da masu kamfanoni masu sarrafa amfanin gona suma su taka muhimmiyar rawa domin a ceto ƙasannan daga yunwa da fatara da talauci da rashin aikinyi ga matasa.

Shirin nan mai ɓangarori masu yawa na samar da kuɗaɗe ga ‘yan ƙasa domin gudanar harkokin kasuwanci da sana’o’i daban-daban yana da kyau, abu daya kamata ayi shine, cusawa ‘yan ƙasa tun daga tushe kishin ƙasa da kishin kansu da kuma al’ummarsu, mu sani shi wannan shiri an zo dashi ne domin ya zama wani mabuɗin arzikin ƙasa ga ‘yan ƙasa, saboda haka sai kowa da kowa ya bada ta sa gudunmawar ganin an cimma burin da Bola Ahmad Tinubu ya ɗauka kan san a sadaukar da kai riƙon amana da gaskiya da tafiiyar da al’amura cikin tsari da biyayya da shugabannin ƙasa, su kuma shugabanni su kasance masu tausayi ga talaka wato mutane na ƙasan-ƙasan da suke karkara da burane.

By ukarofi