•NLC da CHRIceD sun ce akwai rashin tausayi a ƙarin kuɗin
*Ba kowa ƙarin zai shafa ba, cewar gwamnati
*Ƙarin zai haifar da satar wuta, inji tsohon jami’in NERC
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A daidai lokacin da al’ummar Nijeriya ke fama da raɗaɗin tashin farashin kayayyakin masarufi da tsadar rayuwar da, sai ga shi Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) ta fitar da sanarwar amincewa da ƙarin kuɗin wutar lantarki ga kwastomomin da ke ƙarƙashin rukunin samun wuta na Band A, wato waɗanda suka fi samun wutar lantarki.
A wani taron manema labarai a wannan Larabar a Abuja, Mataimakin Shugaban NERC, Musliu Oseni, ya ce, “ƙarin kuɗin zai mayar da kuɗin ma’aunin wutar lantarki na kilowatt ɗaya duk sa’a daga Naira 66 da ake biya a yanzu zuwa Naira 225.
“Mun gano cewa waɗanda ke qarqashin tsarin Band A ne ke samun wutar lantarkin na sa’o’i 20 a kullum.”
Oseni ya ce, waɗannan kwastomomi suna wakiltar kashi 15 cikin ɗari na masu amfani da wutar lantarki miliyan 12 a ƙasar.
Ya ƙara da cewa, hukumar ta sauke wasu kwastomomin da ke kan tsarin samun wuta daga Band A zuwa Band B.
Wannan ya zama wajibi ne saboda rashin cika sa’o’in da ake buƙata na wutar lantarki da kamfanin rarraba wutar lantarkin ke samarwa.
“A halin yanzu muna da fidoji 800 da aka kasafta a matsayin Band A, amma yanzu za a rage su zuwa ƙasa da 500.
“Wannan yana nufin cewa kashi 17 ne cikin 100 suka cancanci zama masu amfani da matsotsar Band A.
A baya dai Kamfanin Dillancin Labarai na Bloomberg ya ce za a ba kamfanonin wutar lantarki damar kara farashin wutar lantarki zuwa N200 ($0.15) a kowace kilowatt daga naira 68 ga masu amfani da wuta a birane daga wannan watan.
Bloomberg ya bayyana hakan ne a ranar Talatar da ta gabata.
Ya ruwaito cewa, gwamnati ta ce waɗannan kwastomomi su ne masu wakiltar kashi 15% na al’ummar qasar da ke amfani da kashi 40% na wutar lantarkin da ake samarwa.
Waɗansu majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa da ke da masaniya kan lamarin sun ce za ayi hakan ne da nufin janyo hankulan sabbin masu zuba jari a harkokin wutar lantarki.
Masu fafutika kan inganta wutar lantarki a Nijeriya sun bayyana wa wakilinmu cewa wannan lamari ya zo musu da kaɗuwa, inda suka ce, ba zai tava yiwuwa ‘yan Nijeriya su jure matakin cire tallafin wutar lantarki kai tsaye ba, baya ga cire tallafin man fetur, lamarin da ya jefa rayuwar ‘yan ƙasar cikin tasku.
Da mu ka tuntuɓi Babban Manajan Hukumar kula da harkokin Jama’a a NERC, Dakta Usman Arabi a ranar Talata, bai amsa kiran mu ba kuma bai amsa saƙonnin tes ɗinmu ba.
Bloomberg ya ce Bayo Onanuga, mai magana da yawun fadar shugaban qasar ya ce, “Masu ruwa da tsaki a hukumar NERC za su yi wa ‘yan Nijeriya jawabi idan sun kammala tattaunawa da kamfanonin rarrabawa da samar da wutar lantarki a ƙasar”.
Ya ce “Fadar Shugaban Ƙasa ba za ta iya cewa komai a kan wannan matakin ba. Bangaren wutar lantarki na cikin mawuyacin hali.”
Mambobin ƙungiyoyin fararen hula sun bayyana damuwarsu kan rahotannin baya-bayan nan da ke nuni da cewa gwamnatin tarayya na shirin ruɓanya farashin wutar lantarki kusan sau uku nan da ‘yan makwanni.
A nasa jawabin, babban daraktan Cibiyar Kula da ‘Yancin Ɗan Adam da Ilimin Jama’a (CHRIceD) Kwamared Ibrahim M. Zikirullahi ya bayyana cewa, ƙara farashin kilowatt ɗin wutar lantarki zuwa Naira 200, maimakon Naira 68 a halin yanzu a Nijeriya na nuna cewa gwamnatin Tinubu ba ta tausayin talakawan ƙasar nan.
Akwai rashin tausayi a ƙarin kuɗin wutar lantarki da gwamnati ta yi — NLC
Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya NLC da waɗansu ƙungiyoyin fararen hula sun yi tir da ƙarin kuɗin wutar lantarki ga masu amfani da tsarin wuta mai daraja ta ɗaya wato Band A.
A zantawarmu da wasu daga cikin ’yan rajin kawo canji da kuma ’ya’yan ƙungiyar NLC, sun ce duk dalilan da jami’an gwamnati suka bayar kan ƙarin kuɗin ba hujjoji ba ne.
A cewarsu, ko a ƙasashen da aka ci gaba, ana tallafa wa wasu ɓangarori kamar man fetur da wutar lantarki.
Shugaban yaɗa labarai a hedikwatar NLC, Benson Upah, ya ce ƙungiyar ta su za ta ɗauki matsaya kan mummunan ta’asar da aka yi na ƙarin kuɗin wuta.
Benson ya ce, za su sanar da matsayarsu idan masu ruwa da tsaki a ƙungiyar sun zauna.
“Shawarar da gwamnati ta yanke ba iya rashin tausayi ba ne, shawarace mai muni ƙwarai da gaske.”
Ya ce “wannan hukunci zai ƙara wa ’yan Najeriya wahalar da suke ciki. Sannan kuma zai ƙara gigita harkokin kasuwanci a ƙasar nan.
“Abin da in aka yi wasa zai kore masu saka hannun jari daga ƙasashen ƙetare a Nijeriya.
Ya ƙara da cewa, “Mutanen da za su ci riba daga wannan tashin hankali da jama’a za su shiga su ne Bankin Duniya da Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF.
“Abin tausayi! Za mu dawo gare ku a kan wannan batun nan gaba kaɗan, bayan masu ruwa da tsaki a kan wannan mataki na ƙungiyarmu sun zauna.”
A nasa ɓangaren, daraktan ƙungiyar ActionAid Nigeria, Andrew Mamedu, ya ce “ƙarin wani ƙarin nauyi ne mai wuyar sauke wa aka ɗora a wuyan ’yan Nijeriya, musamman masu kiaramin ƙarfi da kuma masu ƙananan sana’o’i.
Ƙarin kuɗin zai haifar da satar wuta da rashawa
Wani tsohon shugaban NERC, Sam Amadi, ya ce ƙarin kuɗin wutar lantarki zai haifar da satar wutar kuma zai ƙarfafa rashawa da almundahana a sashen.
Da yake magana a gidan Talabijin na Trust, Amadi ya ce, “Idan ka ƙara kuɗin wutar lantarki zuwa matakin da mutane ba za su iya ba, hakan zai ƙara janyo satar wuta ta bayan fage, cin hanci da rashawa, kuma a ƙarshe, ma’aikatu za su yi asara fiye da kima.
Sannan kuma, “eh gaskiya ne akwai kwakkwaran dalili na ƙara kuɗin harajin saboda matsalar kuɗin da ake samu da kuma ƙarin farashin iskar gas da za a sayar wa kamfanonin samar da wutar lantarki.”
