Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, ta yi ƙarin haske akan dalilan kai ƙarar gwamnonin ƙasar 36 da kuma ministan birnin tarayyar Abuja gaban kotu.
Ƙungiyar ta ce ta shigar da wannan ƙara ne saboda rashin bayar da bayanai kan yadda gwamnonin jihohin Nijeriya 36 da ministan Abuja, suka kashe kuɗaɗen da suka ciyo na bashin naira tiriliyan kusan shida, da kuma sama da dala billiyan 4 da rabi, ba tare da bahasi ba.
SERAP ta buƙaci kotun da ta gayyaci hukumar EFCC da ICPC domin ƙaddamar da bincike kan yadda aka kashe basusukan da gwamnonin suka karɓo.
Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaai da cin hanci a Nijeriya ta ce ta shigar da karar ne a ranar juma’ar makon da ya gabata a babbar kotun tarayya da ke Abuja.
SERAP ɗin ta ce, ta shigar da ƙarar ne bayan gazawar gwamnonin wajen yi wa al’ummar su bayanin yadda suka kashe basusukan da suka karvo da wajen da aka aiwatar da auikin da aka karvo bashin dominsu.
Kolawole Oluwadare mataimakin daraktan ƙungiyar ta SERAP ya bayyana cewa bayani, “Mun je kotu ne don a tursasa, tare da bai wa gwamnonin da ministan birnin Abuja umarnin bayar da bayani na yarjejeniyar da suka cimma da waɗanda suka basu bashin. Sannan mun buƙaci a gayyato hukumar yaqi da cin hanci da rashawa ta EFCC, da hukumar yaƙi da masu yiwa tattali arzikin ƙasa ta’annati ta ICPC domin su ƙaddamar da bincike kan yadda aka ciwo bashin. Yan Nijeriya musamman na jihohin da aka ciwo bashin na da haqqin sanin yadda aka yi da kuɗaɗen, da yadda aka kashe su, da inda aka kashe su. Saboda haka bayyana irin waɗannan bayanai haƙƙi ne a kan masu mulki.’’
“Waɗannan ƙararraki da SERAP ke shigarwa ba wai tana yi bane domin ƙashin kanta, tana yi ne don al’umma dogaro ga kundin mulkin Nijeriya da ya bayar da yancin neman bayanai. Don haka, wannan jan aafa da ake gani na fara sauraron ƙararakin da muke shigarwa na da alaƙa da jan ƙafa da ake guskanta a ɓangaren shari’ar ƙasar. A ce sai an kai shekara uku da shigar da ƙara sannan za a fara sauraron ta, abu ne mai cike da damuwa.’’
Kolawole Oluwadare ya kuma jaddada cewa SERAP ba za ta tava yin ƙasa a gwiwa ba saboda irin waɗannan ƙalubale.
Wanann dai na zuwa ne tun bayan da hukumar kula da basusuka ta Nijeriya ta fitar da rahoton basusukan da ake bin jihohin ƙasar 36, da baban birnin tarayayar ƙasar Abuja da ya kai naira tirliyan 5.9, da wanda siuka karbo a waje da ya kai dala biliyan 4.6.
Sai dai kawo yanzu ba a tsayar da ranar da za a fara saurarar ƙarar da SERAP ɗin ta shigar ba.
