Muna zaune lafiya da sauran ƙabilu – Ƙungiyar Mahautan Legas

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Mahauta a Jihar Legas, wadda ta ke zaune a Mayankar Shanu Abbatuwa a Ƙaramar Jukumar Okoba Agege da ke Legas, Alhaji Abdullahi Ahmed ya bayyana cewa, su na zaune lami lafiya tare da sauran ƙabilu mahauta masu gudanar da harkokin sana’ar fawa a Legas da kewayanta gabaɗaya.

Shugaban ƙungiyar ya yi wannan tsokaci ne a ofishin ƙungiyar da ke Okoba agege jim kaɗan bayan tashi daga taron su na ƙungiyar mahautan Legas da kewayanta bakiɗaya.

Wakilin Jaridar Manhaja ya tattauna da shugaban ƙungiyar a game da nasarorin da suka samu ta fannin sana’arsu a Legas, inda shugaban ya ce, sun samu nasarori masu yawa a sana’ar fawa.

Ya ƙara da cewa, kaɗan daga cikin nasarorin da suka samu sune farko dai sun samu zaman lafiya tare da haɗin kawunan junansu sannan sun duƙule sun haɗe sun zama tsintsiya maɗaurinki zaya da sauran ƙabilu mahautan jihar, sannan luma harkokin fawa suna tafiya bakin gwargwadon hali da sauran makamantansu.

Ya cigaba da cewa, sai dai wannan al’amari da ya zo na canjin kuɗin Nijeriya da ya zo ya dama harkokin dukan wani mai juya kuɗi ta fannin kasuwanci, ya ce, al’amarin da ya sanya harkokin mahauta da sauran ’yan kasuwa suka yi tsaye a daidai wannan lokaci.

Ya ce, saboda haka sana’ar fawa sai dai haƙuri tare da godiyar Allah, amma a halin da ake ciki yanzu komai ya lalace ba kamar wancan shekarun baya da suka gabata ba da za ka sayi shanu ka raba wa mahauta su yanka ka jira su haɗo maka kuɗinka tare da ribarka gabazaya.

Ya cigaba da cewa, amma yanzu hakan ya gagara saboda komai ya yi kuɗi ga kuma matsalolin zamani da suka baibaye sana’ar fawa.

Ya ce, amma ta ɓangaren halin zamantakewarsu da sauran ƙabilu mahautan Legas waɗanda suka haɗa da Hausawa Yarabawa da Ibo da sauran ƙabilu masu sana’ar fawa suna zaune lami lafiya a Legas.

A cewarsa tun da komai tare suke yi haka kuma duk wanda ya yi laifi Bahaushe ko Bayarabe ko Ibo za su taru suyi masa hukuncin da ya kamata suyi masa babu wata matsala a tsakanin su.

Ya nuna rashin jin daɗinsa a game da matsalolin da canjin kuɗin Nijeriya ya kawoma mahauta da sauran ’yan kasuwa a Nijeriya, inda a nan ma ya cigaba da cewa, haƙiƙa wannan canjin kuɗi ya zame wa ’yan Nijeriya gabaɗaya matsala ba wai ’yan kasuwa kaɗai ba, saboda harkokin ƙasar gabaɗaya sun tsaya cik ta dalilin wannan al’amari.

A cewarsa, saboda kowacce irin sana’a kake yi wannan canjin kuɗi ya shafeka tun da zaka je banki wuni uku baka samu kashi ɗaya daga cikin kaso goma na kuɗin da ka kai banki domin a canja maka su zuwa sabbj ba.

A ƙarshe, ya ce, akan haka yake son ya shawarci shugaban ƙasa mahammadu Buhari da ya dubi Allah ya dubi Annabi ya kawo ƙarshen waɗannan matsalolin canjin kuɗi a Nijeriya da suka addabi ’yan kasuwar Nijeriya da talakawa da sauran al’ummar ƙasar bakiɗaya.

By Editor