
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero wanda gwamnatin Jihar ta sauke daga karagar mulki, ya gayyaci tawagar hakiman Jihar zuwa bikin wasan doki na durbar da ake gabatarwa a lokutan Sallah da ma wasu bukukuwan.
Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi ya fitar da sanarwar a wata takarda dake ɗauke da sa hannunsa a ranar Talata inda take umurtan dukkan masarautun Jihar da su halarci taron da Hakimai da masukunta da kuma mawakansu a lokacin bikin sallah babba.
Bayanin takardar, ya ƙara da cewa tana kira ga dukkan Hakiman masarautu da su hallara a fadar Aminu Ado Bayero dake Nasarawa a ranar asabar, 15 ga watan Yuni da misalin karfe 11 na safe domin cigaba da karɓar umurni daga fadar.
