Majalisar Tarayya zata karɓi ƙudurin dokar sabon mafi ƙarancin albashi nan ba da jimawa ba- Tinubu

Spread the love

Shugaba Tinubu ya ba da tabbacin cewa nan bada jimawa ba zai tura ƙudurin mafi ƙarancin Albashi zuwa Majalisar Tarayya.

Ya faɗi haka ne a yayin jawabin sa na ranar dimukraɗiya a ranar 12 ga watan Yuni.

” a cikin mutuntawa tare da ƙungiyoyin Ƙwadago, mun tattauna a kan sabon tsarin albashi mafi ƙaranci. Nan ba da jimawa ba zamu aika da ƙudurin zuwa majalisa domin ya zama doka na shekara biyar ko ƙarancin haka”

Ya ƙara da cewa babu ko ɗaya cikin jagororin Ƙungiyar Ƙwadago da aka tsangwama ko aka kama a dalilin yajin aikin da suka yi ranar 3 ga watan Yuni.

A ranar juma’a bakwai ga watan Yuni duka ɓangarorin biyu( ɓangaren gwamnati da Ƙwadago) sun miƙa sakamakon tattaunawar su ga Shugaban Ƙasa domin ya yanke hukunci sannan ya tura ƙudurin zuwa Majalisar Tarayya.

By ukarofi