Ya manin Kirifto Karansi yake aiki?

Spread the love

Daga ALIYU ƊAHIRU ALIYU

Idan zan turo maka kuɗi ta banki zuwa asusun ajiyarka na banki ai bankin zai ɗauki ladan aiki ko? A ladan aikin nan za a ba wa ma’aikata albashi waɗanda su ne suka buga stamfi/tambari kuma suka danna kwamfuta har kuɗin ya isa. To kamar haka manin yake aiki a Kirifto Karansi amma ba sak ba.
Asali shi manin yana nufin yadda mutane suke amfani da kwamfuta don tabbatar da duk wata “hada-hadar kuɗi” (cinikayya ko tafiyar sakonni) da yake “blockchain”, wanda shi bulokcan (block da chain) na nufin gamayyar ma’adanai (decentralized databases) da suke haɗe da juna kuma suke adana duk wani bayanan abin da ke faruwa a harkar Kirifto. Duk wanda yake hada-hadar kuɗi a Kirifto to yana da wannan “block” din da yake da kwafin duk abin da yake faruwa, shi ya sa ake kiransa da “decentralized” ma’ana ba a guri ɗaya sakon yake tattara ba.
Mai yin “manin” yana shiga ne domin a tabbatar duk abin da ake a Kirifto Karansi dai-dai yake. Hakan shi ake kira da “validation”. Shi wannan ‘validation’ ɗin yana buƙatar kwamfuta ta iya amsa wani lissafi mai zurfi ne (complex mathematical puzzles). To shi mai yin manin aikinsa kenan ya ga ya amsa wannan “puzzle” din domin a tabbatar da cewa hada-hadar kuɗi a Kirifto Karansi dai-dai yake a bulokcan. Idan ya yi sa’ar yin hakan to za a bashi ladan aiki. To ta haka masu manin suke samun kudi.
To, amma asali manin da manyan kwamfutoci ake yi irin samfurin waɗanda ake kira da “supercomputers” da suke ɗauke da “Application-Specific Integrated Circuits” (ASIC) idan za a yi na Bitkoyin ko kuma Graphics Processing Unit (GPU) idan za a yi na Ethereum da sauran Kirifto Karansi daban-daban. Kuma suna da matuƙar jan wuta da nauyi a yayin da suke aikinsu. Wannan yana da wuya ko a ƙasashen da ba a ɗauke wuta.
Maimakon haka, sai aka gano cewa a dinga haɗe ƙananun kwamfutoci na duniya da wayoyi domin a samar da babbar kwamfuta guda ɗaya da za ta dinga manin. Wannan shi ake kira da “mining pool”. Ta irin haka ne ake manhajoji na waya da idan ka shiga to kai ma za a haɗa da wayarka ko kwamfutarka wajen a amsa wannan “mathematical puzzle” ɗin.
Idan an yi nasara to za a raba ladan aikin da kai wanda yana zuwa ne a matsayin “Kirifto Karansi”. Shi kuma ba zai yi maka amfani ba sai dai idan abin canji kamar Binance da ByBit sun karɓa sai ka canja shi zuwa Dalar Amurka (USDT) ka siyar ka karɓi Naira.
To ka ji yadda ake manin na Kirifto Karansi.

Aliyu Ɗahiru Aliyu masani ne kuma mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum musamman ma na siyasa da tattalin arziki.

By ukarofi