Sufeta Janar ya dakatar da ƙarin girma na musamman a hukumar ‘Yan Sanda

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Sufeta Janar na hukumar ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya sanar da dakatar da tsarin ƙarin girma na musamman da ake yi wa jami’ansu inda ya ce hakan na haifar da rauni da kawo cikas ga ƙoƙarinsu wajen gudanar da ayyukansu.

Kayode ya bayyana hakan ne a yayin bikin girmama manyan jami’ai 15 da hukumar ta ƙara wa girma a Abuja.

Kayode, ya bayyana alhininsa kan yadda wasu ma’aikatan ke kamun ƙafa wajen neman waɗannan muƙaman, dan haka ya ce duk wanda aka kama da yunkurin haka, to za’a hukunta shi.

Ya kuma ƙara da cewa, idan akwai buƙatar yin sauyi ga tsarin a nan gaba, to zasu yi hakan, sannan ya kuma gargaɗi jami’ai masu neman canjin wuraren aiki inda ya ce za’a hukunta duk wanda aka samu da laifin haka.

By Babaji