Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Yemi-Esan za ta yi ritaya a Agusta

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugabar Ma’aikatan Gwamnati Tarayya, HoCSF, Dakta Folasade Yemi-Esan, za ta yi ritaya a ranar 14 ga Agusta, 2024.

Daraktan Sadarwa na HoCSF, Mohammed Ahmed, ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin tattaunawa da wakilan kafafen yaɗa labarai don tunawa da makon ma’aikata na 2024.

A cewarsa, Yemi-Esan za ta cika shekara 60 a ranar 14 ga watan Agustan wannan shekara, shekarun ritayar dole ga ma’aikatan gwamnati a manyan ma’aikatu da sauran hukumomi.

Idan za a iya tunawa, an naɗa Yemu-Esan ne a ranar 18 ga Satumba, 2019, bayan da aka cire tsohuwar shugabar HoCSF, Winifred Ekanem Oyo-Ita.

Yemi-Esan, wadda aka ƙaddamar a ranar 4 ga Maris, 2020, ta yi aiki a matsayin Babbar Sakatare na Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur.

By ukarofi