Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gamayyar ƙungiyoyin fararen hula ta Kano wato Kano Civil Society Forum (KCSF) ta rantsar da sabbin shugabannin da za su gudanar da ƙungiyar bayan shekara 11 a ƙarƙashin tsarin shugabancin riƙo.
Jaridar Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa taron rantsarwar ya gudana ne a cibiyar ‘yan jarida ta NUJ da ke Kano a ranar Talata da ta gabata.
Sabon Shugaban gamayyar Muhammad Bello, wanda kuma shi ne shugaban cibiyar binciken ƙirƙire-ƙirƙire da ci gaban Afirka wato African Center For Innoɓatiɓe Research and Deɓelopment ya ce ya na mai gode wa ƙungiyar bisa wannan aiki da aka ba shi, kuma ya yi kira da a haɗa kai a tsakanin mambobin domin ciyar da manufofin ƙungiyar gaba.
Ya ce ƙungiyar tuni ta fara tuntuɓar masu ruwa da tsaki akan harkar shugabanci wajen ganin an warware dukkan matsalolin da su ke addabar ƙungiyar.
“Za mu yi iya yin mu don muna mun ja hankalin gwamnati zuwa ga abubuwan da suka shafi ci gaban al’umma,” inji Kwamared Bello.
Kazalika an rantsar da Fatima Musa ta Bridge Comment Afirika initiatiɓe a matsayin Mataimakiyar shugabar kungiyar ta 1, yayin da Kabiru Ibrahim ya zama mataimakin shugaban na 2. Sai kuma Salisu Yusuf shugaban kungiyar kare al’umma ta Kano Social Protection Platform, a matsayin Sakatare, sannan kuma da Aminu Sani Muhammad a matsayin mataimakin sakatare janar.
Sauran waɗanda aka rantsar sun haɗa da Maryam Garba a matsayin Ma’aji da Umar Musa a matsayin mai bada shawara kan harkokin shari’a.
