
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ce za a kammala aikin filin jirgin saman Gusau cikin nan da wata uku.
Gwamnan ya faɗi hakan ne a yayin taron buɗe aikin filin jirgin wanda Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya yi a Gusau, babban birnin Jihar a ranar Alhamis da ta gabata.
A wani jawabi daga mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai, Sulaiman Idris, an ƙaddamar da aikin filin jirgin ne domin yin sufuri a cikin gida Najeriya da kuma ƙasashen waje.
Ya ƙara da cewa, aikin zai ci tsawon kilomita 3 zuwa 4 wanda zai dace da sufurin jiragen ƴan kasuwa, sannan kuma za a sanya fiitilun kan hanya da alamu domin ƙawata shi da kuma jin dadin masu zirga-zirga.
Dauda Lawal, ya bayyana cewa gwamnatinsa tana ƙoƙari wajen ganin ta samar da sabuwar Jihar Zamfara ta yadda mutane daga gida da waje zasu ke zuba hannun jari a harkoki daban-daban musamman waɗanda suka shafi kasuwanci da makamantansu.
