Trump ya yi alƙawarin katin ɗan ƙasa ga ƴan ƙasar waje da suka yi difuloma a Amurka

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ɗan takarar jam’iyyar ‘Republican’ kuma tsohon shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump ya yi alƙawarin mallaka wa dukkan ƴan ƙasar waje katin zama ɗan ƙasa matukar mutum ya yi karatun matakin difuloma a ƙasar.

Trump, ya faɗi hakan ne a wata hira da ƴan jaridu, jim kaɗan bayan babban abokin hamayyarsa kuma shugaban ƙasar na yanzu, Joe Biden ya shelanta cewa za’a ƙwace matsayin ƴancin zama ɗan ƙasa ga duk waɗanda suka auri ƴan Amurka da ba ƴan ƙasa ba a ƙoƙarinsa na kawo ƙarshen magance matsalar zama ɗan ƙasa ba bisa ƙa’ida ba da wasu da dama ke yi a ƙasar.

Trump ya ƙara da cewa, katin wanda aka yi wa laƙabi da ‘green card’, za’a bai wa duk wanda ya/ta yi karatu a kwaleji da ya kai matakin mallakar kwalin difuloma da kuma waɗanda suka samu yin sama da wannan, kamar masu digirin-digirgir.

By Babaji