Rikicin Masarautar Kano: ’Yan sanda sun sake gargaɗin masu tada zaune tsaye

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya, reshen Jihar Kano ta roƙi jama’a su zauna lafiya a lokacin da ake dakon hukuncin Babbar Kotun Tarayya kan rikicin sarautar jihar.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa ya fitar a Kano ranar Alhamis.

Abdullahi Kiyawa ya nanata ƙudurin hukumar na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Kakakin ‘yan sandan ya kuma gargaɗi duk wani mai yunƙurin tayar da zaune tsaye bayan hukuncin kotu ya gaggauta canja tunani.

“Tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, rundunar ‘yan sanda za ta tabbatar da dokar haramta zanga-zanga da wasu tarurruka da gwamnatin Kano ta yi.”

“Duk wanda ya yi kunnen ƙashi zai ɗanɗana kuɗarsa domin za a girke ƙarin dakarun tsaro da za su tabbatar da bin doka da oda.

“Muna kira ga al’umma su ba jami’an tsaro haɗin kai kuma su taimaka mana da sahihan bayanai don mu gudanar da aikinmu na tabbatar da zaman lafiya,” inji Abdullahi Kiyawa.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma shawarci sauran jami’an tsaron da ba na gwamnati ba kamar ‘yan banga da mafarauta su guji shiga harkokin tsaro.

By ukarofi