Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ya bayyana Gwamnatin Tarayya na shirin mayar da wasu otel ɗin Zaria (Zaria Hotels) da ke Jihar Kaduna zuwa ajujuwa da kuma ɗakunan kwanan ɗalibai na Kwalejin Fasahar Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAT).
Keyamo ya sanar da samun otel-otel ɗin Zaria a matsayin wani ɓangare na walwalar NCAT, yayin wani rangaɗin sanin makamar aiki a ranar Laraba.
Ya ƙara da cewa, wannan yunƙuri na da nufin bunƙasa cigaban kwalejin.
“NCAT ta kasance cibiya mafi kyawu na sufurin jiragen sama a Nijeriya da Afirka ta Yamma. Filin da muke da shi a nan ya isa a faɗaɗa kwalejin, ”inji Keyamo.
“Duk da haka, mun kuma mallaki wasu otel-otel na Zaria a matsayin habyar faɗaɗa kwalejin, inda za mu ƙara da wanda muke da shi a ƙasa. “
Ministan ya baiwa hukumar kula da kwalejin tabbacin ci gaba da ƙoƙarin gwamnati na haɓaka wuraren da ake buƙatar ingantawa.
Ya kuma yi watsi da jita-jita game da canja wa kayan kashe gobara na kwalejin da sauran kayan aiki wuri, inda ya ce bai da tushe balle makama.
“Babu wani abu kamar haka; idan muka yi, ina za mu kai shi? NCAT ita ce cibiyar horar da jiragen sama; ’yan ɓarna ne ke yaɗa wannan jita-jita,” inji Keyamo.
Shugaban riƙo na NCAT, Mista Joseph Imalighwe, ya bayyana godiya ga ministan bisa ziyarar da ya kawo wa kwalejin.
